Jama’atu ta agaza wa ’yan gudun hijira 1,200 a Gombe

kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Gombe a karkashin jagorancin Mataimakin Shugabanta na kasa, kuma Shugabanta na Jihar Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, ta raba kayan agaji ga ’yan gudun hijirar rikicin Boko Haram da ke jihar. A jawabin Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, ya ce an aiko da buhuna […]

Jama’atu ta agaza wa ’yan gudun hijira 1,200 a Gombe
Jama’atu ta agaza wa ’yan gudun hijira 1,200 a Gombe

kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Gombe a karkashin jagorancin Mataimakin Shugabanta na kasa, kuma Shugabanta na Jihar Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, ta raba kayan agaji ga ’yan gudun hijirar rikicin Boko Haram da ke jihar.

A jawabin Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, ya ce an aiko da buhuna dubu daya da dari biyu ne na shinkafa da gallan-galan din man girki don raba wa ’yan gudun hijirar kuma ya kaddamar da shirin da ba mutum biyar a fadarsa inda sauran za su karbi nasu kason daga baya, kafin a je kananan hukumomin da aka dauki sunayensu su karba a can.
Sarkin ya ce an bi tsarin daukar sunaye a kananan hukumomin da suke zaune aka yi rijista aka ba kowannensu kati kuma sai wanda yake da wannan kati za a ba tallafin domin kada a samu rudani a lokacin raba kayan.
Babban Sakataren kungiyar a jihar Alhaji Saleh danburam Magajin Malam, ya ce sun zakulo ’yan gudun hijirar ne a karkashin wani karamin kwamiti da Sarkin ya nada inda suka zagaye kananan hukumomi shida na jihar da aka san akwai ‘yan gudun hijirar.
daya daga cikin wadanda suka samu tallafin mai suna Muhammad Isa Isge, wanda ya fito daga karamar Hukumar Damboa a Jihar Borno da ya yi jawabin godiya a madadin ’yan gudun hijirar ya yi Sarkin da daukacin al’ummar Jihar Gombe godiya kan taimakon da suke ba su.
MuhammadIsge, ya ce tallafin da aka ba su ya zo a lokacin da suke tsananin bukatarsa wato lokacin azumin watan Ramadan.
Kayayyakin da aka ba su sun hada da din shinkafa da man girki, kuma an zakulo ’yan gudun hijirar ne daga kananan hukumomin Akko da Gombe da Funakaye da Kwami da Nafada da kuma Yamaltu Deba.