Jama’atu ta gargadi malamai a kan sukar juna a lokacin Tafsiri

kungiyar Jama’atul Nasril Islam ta kasa (JNI) ta gargadi malaman da za su gudanar da wa’azi lokacin Tafsirin watan Ramadan na ban kan su guji sukar juna da furta kalaman da za su jawo tashin hankali a tsakanin jama’a. Babban Sakataren kungiyar Sheikh Khalid Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar […]

Jama’atu ta gargadi malamai a kan sukar juna a lokacin Tafsiri
Jama’atu ta gargadi malamai a kan sukar juna a lokacin Tafsiri

kungiyar Jama’atul Nasril Islam ta kasa (JNI) ta gargadi malaman da za su gudanar da wa’azi lokacin Tafsirin watan Ramadan na ban kan su guji sukar juna da furta kalaman da za su jawo tashin hankali a tsakanin jama’a.

Babban Sakataren kungiyar Sheikh Khalid Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da sakamakon rahoton azumin bara a lokacin taron da Jama’atu ta shirya a Kaduna ranar Lahadin da ta gabata.
Sheikh Khalid ya nuna damuwa kan abin da ya faru a lokacin azumin bara, inda ya ce wasu malamai sun yi amfani da lokacin wajen sukar juna. Ya ce a lokacin tafsirin bara “Akwai malaman da kalamansu na iya janyo rikici kuma gaskiyar zance shi ne akwai kalamai da wasunsu suka yi wanda idan da ba Musulmi ya yi su ba, da an samu rikici. daya daga cikin irin Tafsirai masu hadari da suka bayyana shi ne na ’yan Shi’a wanda kuma aka rika yadawa ta gidajen rediyo da talabijin, kuma akidunsu na ci gaba da yaduwa a cikin al’ummar Musulmi,” inji shi.
An wurin taron Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Jamatu, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya raba buhun shinkafa dubu 18 ga ’yan gudun hijira daga jihohin Borno da Adamawa da Yobe da Kaduna da Kano da Gombe da kuma Bauchi.ý
Sarkin Musulmin ya ce kayayyakin abinci za su taimaka wajen rage radadin da ’yan gudun hijirar ke fukanta, sai ya gargade su da kada su kuskura su sayar da abincin domin a cewarsa an ba su ne domin rage masu radadin da suke ciki.
Sarkin Musulmi ya ce yana fatan abincin zai taimaka musamman yanzu da watan azumi ke kara kusantowa.
Aminiya ta ga an loda buhunan shinkafa da sauran kayan abincin a cikin rokoki 15 domin kaiwa jihohin da aka ambata.