Jama’atu ta horar da mutum 313 sana’o’i a Jigawa

Kungiyar Jama’atu ta kasa reshen Jihar Jigawa ta bukaci Gwamnatin Jihar Jigawa da ta taimaka mata da filin da za ta gina sakatariyarta a garin Dutse.  Wannan kiran ya fitone daga bakin Wamban Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a wajen wani taro da uwar kungiyar ta yi a ranar Asabar din makon jiya a garin […]

Jama’atu ta horar da mutum 313 sana’o’i a Jigawa

Kungiyar Jama’atu ta kasa reshen Jihar Jigawa ta bukaci Gwamnatin Jihar Jigawa da ta taimaka mata da filin da za ta gina sakatariyarta a garin Dutse. 

Wannan kiran ya fitone daga bakin Wamban Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a wajen wani taro da uwar kungiyar ta yi a ranar Asabar din makon jiya a garin Dutse. Haka zalika ya bukaci Gwamnatin Jihar ta sama wa ‘ya’yan kungiyar gurabu a cikin ayyukan Gwamanatin Jihar.

Ya kuma nuna takaicinsa game da rashin abin hawa da kungiyar za ta rika aiwatarda ayyukanta kai tsaye, don haka ya bukaci Gwamnatin Jihar ta sama wa kungiyar motoci guda biyu: daya ta daukar malaman da suke zagaya wa’azi da kuma ta daukar ‘yan agaji. 

Ya kuma nemi hadin gwiwar Gwamnatin Jihar da shugabannin kananan Hukumomin Jihar wajen basu goyan baya a aikin dashen itatuwa da kungiyar take aiwatarwa a fadin Jihar a kokarinsu na kare kwararowar Hamada. 

Alhaji Aminu ya kuma shawarci Gwamnatin Jihar ta rika daukar nauyin ‘ya’yan kungiyar wajen horar da su dabarun aikin tsaro domin inganta zaman lafiya a fadin Jihar ta Jigawa, sannan kuma a rika shigar da ‘ya’yan kungiyar cikin wadanda za su rika taimakawa alhazai a kasa mai tsarki a lokacin aikin hajji.

Ya ci gaba da cewa yanzu haka kungiyar ta ba wa maza da mata mutun 313 horo a kan sana’oin hannu da suka hada da yadda ake yin sabulun wankin mota da manshafawa da hummara da sabulun da turaren daki domin al’umma su zama masu dogaro da kansu. 

Sannan sun raba tufafi sabbi ga dalibai 30 da aka zabo daga makarantun tsangaya guda 4 daga cikin makarantun tsangayar da ke yankin karamar Hukumar Dutse 

Da yake mayar da nasa jawabin a madadin Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammed Inuwa Tahir ya ce sun ji dukan koke-kokensu kuma zai sanar da Gwamnatin Jihar dukan bukatunsu domin ganin an taimaka masu cikin yardar Allah.