Jama’atu ta nemi a kamo masu kashe malaman Musulunci a kasar nan

kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi Allah wadai da kisan gillar da ‘’yan bindiga suka yi ga fitaccen malamin Musuluncin nan na Zariya Sheikh Awwal Adam Albani tare da neman gwamnati ta kamo masu kashe malamai a kasar nan. A cewar Jama’atu, wannan kisa abin takaici ne matuka don haka sai ta nemi gwamnati […]

Jama’atu ta nemi a kamo masu kashe malaman Musulunci a kasar nan

kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi Allah wadai da kisan gillar da ‘’yan bindiga suka yi ga fitaccen malamin Musuluncin nan na Zariya Sheikh Awwal Adam Albani tare da neman gwamnati ta kamo masu kashe malamai a kasar nan.
A cewar Jama’atu, wannan kisa abin takaici ne matuka don haka sai ta nemi gwamnati ta binciko masu hannu a wannan aika-aika domin hukunta su.
kungiyar ta kuma shaida wa wadanda suka kashe Sheikh Albani cewa koda yake ya bar duniya, amma su sani abin da ya tsaya a kai wato karatun Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) zai ci gaba da wanzuwa a duniya.
A wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Sakataren kungiyar,  Dokta Khalid Abubakar Aliyu da aka raba wa manema labarai a Kaduna, Jama’atu ta ce ta kadu matuka kan kisan gillar da aka yi wa Sheikh Muhammad Awwal Adam,wanda aka fi sani da  Albanin Zariya da matarsa da kuma dansa.
“Abin damuwar shi ne mene ne manufar wannan kisa? Wannan yana nuna mana cewa akwai wani shiri na kisan gilla ga malaman addinin Musulunci a ’yan shekarun nan inda aka fara da kashe Sheikh Ja’afar Mahmud Adam a Kano aka zo kan Malam Umar dan Maishiyya a Sakkwato wadanda har yanzu suke a zukatanmu,” inji sanarwar.
Ta ci gaba da cewa “Har yau, ana ci gaba da kashe malaman Musulunci a jihohin Yobe da Borno da sunan Boko Haram. A yau Dokta Muhammad Nazeef Yunus na hannun jami’an SSS bisa zargin wai dan Boko Haram ne. A haka malaman Musulunci za su ci gaba? Me ya sa masu wannan kisa har yanzu ba a kama su? Kamar kullum muna ci gaba da yin Allah wadai da kakkarfar murya tare da yin kira ga gwamnati ta tabbatar ta kamo wadanda ke da hannun a kisan Malam Albani,” inji shi.
Jama’atu ta kuma yi kira ga Musulmi su kara hakuri kuma su ci gaba da addu’o’i domin neman kariya daga sharrin masu sharri a kasar nan.