Jama’atu ta shawarci malamai masu Tafsirin Ramadan
A yayin da al’ummar Musulmi ke shirin fara azumin watan Ramadan a makon da za mu shiga kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta kasa ta bukaci malamai masu tafsiri a masallatan kasar nan su kauce wa zagi ko aibanta juna a lokacin gudanar da tafsirin. A cewar Jama’atu cikin wata sanarwar bayan taro kan Azumin […]
A yayin da al’ummar Musulmi ke shirin fara azumin watan Ramadan a makon da za mu shiga kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta kasa ta bukaci malamai masu tafsiri a masallatan kasar nan su kauce wa zagi ko aibanta juna a lokacin gudanar da tafsirin. A cewar Jama’atu cikin wata sanarwar bayan taro kan Azumin watan Ramadan, dauke da sa hannun Babban Sakatarenta Dokta Khalid Abubakar Aliyu da kuma Farfesa S.W. Junaidu, ta nemi malaman su yi koyi da karantarwar Alkur’ani da Hadisan Annabi (SAW) wajen gabatar da tafsirin bana. “Akwai bukata matuka ga malamai su kauce wa duk wasu kalamai da ka iya raba kan Musulmi a kasar nan. Yana da kyau a daina batanci ga juna, komai za a yi yana da kyau a yi amfanI da kur’ani da Hadisan Annabi (SAW). Wannan wata na Ramadan akwai bukatar malamai su karantar da mabiyansu kauna da soyayyar juna da hadin kai tare da kira su kasance masu tsoron Allah a duk inda suke, muna fatan dukkan malamanmu za su bi ka’idojin da jama’atu ta gindaya masu domin samun fahimtar juna a wannan azumi,”inji sanarwar. Jama’atu ta kuma bukaci Musulmi da ’yan Najariya su kasance masu tsoron Allah da yi wa juna adalci domin a samu tabbataccen zaman lafiya. kungiyar ta roki masu sayar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su tsauwala wa mutane a lokacin azumin Ramadan. Domin duk wanda ya jikan dan uwansa shi ma Allah zai jikansa. “Haka kuma muna roko ga gwamnati ta amince ta tattauna da ’yan Boko Haram domin kawo karshen kashe-kashe a Arewa,” inji ta.