Jama’atu ta shirya lacca kan yawan mutuwar aure
Reshen mata na kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta Jihar Kano ya shirya taron lacca kan yawaitar mutuwar aure da kuma laifuffukan fyade, wanda aka gudanar a Kwalejin Koyon Shari’ar Musulunci na Aminu Kano a ranar Alhamis din makon jiya.A jawabin maraba, shugabar bangaren mata ta kungiyar Jama’atu, Hajiya Mariya Ali Kote ta ce suna […]
Reshen mata na kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta Jihar Kano ya shirya taron lacca kan yawaitar mutuwar aure da kuma laifuffukan fyade, wanda aka gudanar a Kwalejin Koyon Shari’ar Musulunci na Aminu Kano a ranar Alhamis din makon jiya.
A jawabin maraba, shugabar bangaren mata ta kungiyar Jama’atu, Hajiya Mariya Ali Kote ta ce suna shirya tarurrukan fadakarwa duk shekara ne domin kara tunatar da jama’a kan wasu al’amura da suke addabar jama’a domin ganin ana kawar da su kamar yadda addinin Musulunci ya tsara.
Hajiya Mariya Kote ta bayyana cewa yawaitar mutuwar aure da laifuffukan fyade suna matukar tayar da hankalin jama’a, don haka ne bangaren mata na kungiyar ta Jama’atu Nasril Islam reshen Jihar Kano ya shirya laccar ta yadda za a hada hannu wajen yin gyara, musamman a wannan lokaci da al’amura suke kara tabarbarewa a tsakanin jama’a.
Hajiya Mariya Ali Kote ta ce wajibi ne a rika shirya irin wadannan laccoci domin kara fadakar da jama’a kan yadda za a gyara abubuwan da suke tabarbarewar.
Jihar Sakkwato za ta kafa kamfanin wutar lantarki mai karfin Megawatt 100 daga hasken rana
Daga Nasiru Bello, Sakkwato
Gwamnatin Jihar Sakkwato za ta kafa kamfanin wutar lantarki mai aiki da hasken rana don samar wa jihar wutar lantarki mai karfin megawatt 100, domin a kara bunkasa harkokin kasuwanci da kanana da manyan masana’antu a jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Bashir Garba ne ya fadi haka a lokacin da yake sanya hannu a kan yarjejeninyar amincewa da haka a tsakanin gwamnati da wani kamfanin kasar Chaina mai suna Kunming Engineering Corporation.
Ya ce “A Jihar Sakkwato muna da hasken rana mai yawa wanda ba a komai da shi domin cin gajiyarsa, bayan mun yi magana da kamfanoni da dama kan wannan lamarin gwamnati ta yanke shawarar hada hannu da wannan kamfani domin tsarinsa mai kyau ne kuma wannan shiri mai zaman kansa ne gwamnati za ta bayar da fili da wasu kayan bukata in da kamfanin zai nemi amincewa daga Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta kasa, in aka kammala aikin tare da wanda aka soma a farko na tabbata zai samar da wadatacciyar wutar da ake bukata a Jihar Sakkwato.”