Jama’atu ta yaye sabbin ’yan agaji 205 a Jos
kungiyar ’yan agaji ta Jama’atu Nasril Islam reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato ta yi taron yaye sabbin ’yan agaji 205 a Babban Masallacin Juma’a na garin Jos a ranar Asabar din makon jiya. Shugaban taron kuma Shugaban riko na karamar Hukumar Jos ta Arewa, Dakta danjuma Sanda ya bayyana cewa […]
kungiyar ’yan agaji ta Jama’atu Nasril Islam reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato ta yi taron yaye sabbin ’yan agaji 205 a Babban Masallacin Juma’a na garin Jos a ranar Asabar din makon jiya.
Shugaban taron kuma Shugaban riko na karamar Hukumar Jos ta Arewa, Dakta danjuma Sanda ya bayyana cewa ayyukan agaji suna da matukar muhimmanci ga al’umma. Don haka ya kamata dukkan jama’a su zama ’yan agaji, don su rika taimaka wa juna.
Shugaban wanda Alhaji danjuma Balan Falke ya wakilta, ya yi bayanin cewa babu shakka kungiyar ’yan agaji ta Jama’atu da ke karamar Hukumar Jos ta Arewa ta yi kokari wajen horar da wadannan sabbin ’yan agajin da ta yaye.
Shi ma a nasa jawabin wanda ya yi takarar majalisar wakilai ta tarayya a mazabar Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato Alhaji Sale Bayare ya bukaci masu hannu da shuni su rika taimaka wa ’yan agaji saboda irin ayyukan da suke yi na taimakon al’umma.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban kungiyar ‘yan agajin na kungiyar Jama’atu Nasril Islam reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa Alhaji Suleiman Nayaya ya bayyana cewa, wadannan sababbin ’yan agaji da suka yaye sun yi wata biyu suna karbar horo, kan aikin agaji da yadda ake yin suturar gawa da kuma binne ta.
Ya ce sun horar da su kan irin taimakon da ya kamata su bayar idan matsalar fashewar bam ta auku.
Ya yi bayanin cewa yanzu suna da ’yan agaji 2,870 wadanda suke aiki a kowace mazaba a wannan karamar hukuma.
Ya bukaci sabbin ’yan agajin da aka yaye su rike gaskiya, su yi aiki da abubuwan da aka horar da su.