Jama’atu ta zargi Gwamnatin Jigawa da maida ita saniyar ware
Sakataren kungiyar Jama’atu Nasaril Islam reshen Jahar Jigawa, Alhaji Babangida Hadejia ya yi korafin cewa gwamnatin Jahar Jigawa ba ta damawa da su a fagen aikin addini tun daga kafuwar kungiyar a matakin jaha tun da aka yi jahar zuwa yau. Ya fadi haka ne a wata ganawa da ya yi da wakilimmu a makon […]

Sakataren kungiyar Jama’atu Nasaril Islam reshen Jahar Jigawa, Alhaji Babangida Hadejia ya yi korafin cewa gwamnatin Jahar Jigawa ba ta damawa da su a fagen aikin addini tun daga kafuwar kungiyar a matakin jaha tun da aka yi jahar zuwa yau.
Ya fadi haka ne a wata ganawa da ya yi da wakilimmu a makon jiya, inda ya ce tun da aka yi jahar Jigawa suke neman taimakon gwamnatin jahar domin gina ofishin kungiyar na dindindin a hedkwatar jahar, amma har zuwa yau babu wata gwamnati da ta taimaka masu wajen share wa kungiyar hawayenta.
“Tunda aka yi jahar Jigawa kungiyarmu ta Jama’atu ba ta da ofishi na kanta, tana aiki ne a gidajan haya kuma mun sha gabatar da korafinmu wajen hukuma, amma babu wanda ya saurare mu domin kawo karshen al’amarin.”
Haka kuma Alhaji Babangida ya nuna damuwarsa game da yadda wasu jihohin suke saka ‘ya’yan kungiyar cikin kwamatin aikin Hajji domin taimakawa Alhazai kasa mai tsarki a duk shekara sabanin nan jahar Jigawa.
“Anan Jahar Jigawa ba a daukar ‘ya’yan kungiyar a matsayin ‘yan agaji da za su taimakawa alhazai a kasa mai tsarki kamar yadda sauran jihohi ke yi, gaskiya lamarin akwai abin dubawa akansa matuka domin ita jama’atu ita ce uwar dukkan wasu kungiyoyi na addinin musulinci, amma ba ta amfana daga gwamnatin jahar sai dai a rika taimakawa wasu bangarori amma mu ban da mu ciki.”
Hakazalika Malam Babangida ya nuna damuwarsa matuka game da yadda aka samu yawaitar rarrabuwar kan musulmi saboda abin da ya kira kwadayin neman shugabanci da neman abin duniya da mutane suka zage fiye da son Allah da lahirarsu. Sannan ya hori al’ummar musulmi da su ji tsoron Allah a duk inda suke.
Sai kuma ya yi korafi game da cewa a yanzu haka ma’aikatansu na bin bashin sama da naira miliyan 4 na albashin shekara hudu da ba a biya su ba, haka kuma kudin wuta ya taru akansu sun gaza biya, kuma babu wanda ya biya wa kungiyar dan haka ma ya ajiye kokon bawarsa wajan al’ummar musulmi da sauran ma su fada aji su taimakawa kungiyar.