Jama’atu ta zargi sojoji da kashe Musulmi
kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta kasa (JNI) ta zargi sojojin kasar nan da kashe Musulmi babu gaira babu dalili a wani matakin da ta ce tamkar kokarin kawar da Musulmin kasar ne daga doron kasa.kungiyar ta ce sojojin na aikata kisan gilla a kan Musulmi da ba su san hawa ba, ba su san sauka […]

kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta kasa (JNI) ta zargi sojojin kasar nan da kashe Musulmi babu gaira babu dalili a wani matakin da ta ce tamkar kokarin kawar da Musulmin kasar ne daga doron kasa.
kungiyar ta ce sojojin na aikata kisan gilla a kan Musulmi da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba da sunan yaki da ta’addanci.
Sakatare Janar na kungiyar Dokta Khalid Aliyu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka rarraba ga manema labarai a Kaduna, inda ya zargi jami’an tsaron da kashe Musulmi a jihohin Nassarawa da Yobe da kuma Borno, ya bayyana cewa ana neman a kawar da al’ummar Musulmi ne a cikin kasar ko kuma akalla a rage yawansu.
Sai dai a martanin da ta mayar, hedkwatar tsaro ta sojan Najeriya ta musanta zargin, inda ta ce kalaman Sakatare Janar din za su iya tada hankali.
Kakakin Hedkwatar Tsaron, Manjo Janar Chris Olukolade a cikin wata sanarwar, ya ce dakarun kasar nan za su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da son zuciya ba, kuma rundunar sojan Najeriya za ta ci gaba da ayyukanta na kawar duk wani abu da zai kawo barazana ga tsaron kasar nan.
Sai dai ba wannan ne karon farko da ake zargin sojojin kasar nan da keta hakkin dan Adam ba, wajen aukawa da kashe mutanen da ba su da laifin komai.
A makon jiya ne kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya (Amnesty International) ta nemi kasashen duniya su dauki mataki kan sojoji da ’yan Boko Haram kan yadda suke kashe fararen hula haka siddan.
Sannan a farkon wannan mako ne Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Najeriya ta dora alhakin kisan da aka yi wa wasu matasa a unguwar APO da ke birnin Abuja a kan sojoji da jami’an tsaro na farin kaya (SSS), ba tare da sun aikata wani laifi ba, kuma ba tare da kwakkwarar shaidar suna yunkurin aikata wani laifi ba, inda ta umurce su kan su biya diyya ta Naira miliyan goma-goma ga iyalan kowane daya daga cikin mutum takwas da aka kashe, da kuma Naira miliyan biyar ga kowane mutum da ya samu rauni a harin.
A makon jiya ma sojoji sun kai hari a wata ruga a Jihar Nasarawa inda suka kashe Fulani takwas ba tare da aikata wani laifi ba. Mahukuntan jihar sun ce ba a tuntube su ba a lokacin da sojojin suka aikata wannan danyen aiki, inda shugaban karamar hukumar da lamarinya auku da basaraken yankin suka ce sojojin ba su tuntube su ba, suka yi wannan aika-aika.