JAMB ta bankaɗo ɗalibai 3,000 da suka kammala digirin bogi

An gano waɗanda ke da hannu a lamarin ba su taɓa sanya ƙafa a cikin harabar jami’ar ba.

JAMB ta bankaɗo ɗalibai 3,000 da suka kammala digirin bogi

A ci gaba da ƙoƙarin da take yi na tsarkake tsarin karatun Najeriya, Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i ta Ƙasa JAMB, ta ce ta bankaɗo ɗalibai 3,000 da suka kammala karatu da shaidar digiri ta bogi a faɗin ƙasar nan.

Shugaban Hukumar, Ishaƙ Oloyede, wanda ya bayyana haka a cikin wani rahoto da hukumar ta wallafa, ya ce an gano waɗanda ke da hannu a lamarin ba su taɓa taka ƙafa ba zuwa wani ajin karatu ba.

Oloyede ya bayyana hakan bayan wata ganawa da rukunin kwamitin Shugabannin Jami’o’i na Jiha na Nijeriya (COPSUN) a ofishinsa da ke hedikwatar Hukumar JAMB a Bwari, Abuja.

Ya kuma yi Allah wadai da matakin jami’o’in da suke ba da shaidar shiga jami’a ta bogi da wasu cibiyoyi ke yi ba bisa ƙa’ida ba.

A cewarsa, bayar da shaidar kammala karatun jami’a na bogi da wasu makarantun ke yi ba bisa ƙa’ida abin kunya ga ƙasar.

“Wasu masu shaidar digiri da suka kammala karatunsu ba su taɓa shiga harabar ginin jami’ar ba, saboda yadda matsalar cin hanci da rashawa ta dabaibaye tsarin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “bayar da takardar shaidar kammala karatun jami’a ta bogi a manyan makarantun ƙasar nan ba bisa ƙa’ida ba, abin kunya ne da ke illa ga al’ummar ƙasar.”

Don haka Shugaban ya buƙaci hukumar ta COPSUN da ta tabbatar da cewa sun daƙile shigar da ɗaliban bogi da suke da hannu wanda hakan ke cutar da tsarin da kuma ɓata martabar ƙasar nan.

Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin majalisar wakilai kan ilimi, a watan Disamba 2023, ya umurci hukumar JAMB ta gabatar da jerin sunayen manyan makarantun da suka gudanar da harkokin karatun ba bisa ƙa’ida ba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos