JAMB ta dakatar da ɗalibar da ta sauya sakamako tsawon shekaru uku
Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire UTME, ta soke sakamakon Ms. Ejikeme Joy Mmesoma, sannan ta dakatar da ita daga rubuta sabuwar jarrabawa tsawon shekaru uku. Kakakin JAMB Sunday Fabian Benjamin ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Talata. A ranar Lahadi ne hukumar JAMB ta tuhumi ɗaliba […]
Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire UTME, ta soke sakamakon Ms. Ejikeme Joy Mmesoma, sannan ta dakatar da ita daga rubuta sabuwar jarrabawa tsawon shekaru uku.
Kakakin JAMB Sunday Fabian Benjamin ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Talata.
A ranar Lahadi ne hukumar JAMB ta tuhumi ɗaliba mai shekaru 16, Ms Ejikeme Mmesoma ƴar jihar Anambra da laifin sauya sakamakon jarrabawar UTME daga 249 zuwa 362.
JAMB ta kayyade mafi karancin makin samun gurbin karatu a bana
JAMB: Talata sakamakon jarabawar 2023 zai fito
Hukumar JAMB ta ce ta samu labarin sauya sakamakon ne bayan da kafafen yaɗa labarai suka wallafa cewa Ms Mmesoma ta samu tallafin karatu na Naira miliyan uku sanadiyyar sakamakon da ta ce ta samu.
Ɗaliba ta musanta
Sai dai Ms Mmesoma ta saki bidiyo a soshiyal midiya inda ta musanta wannan tuhumar da JAMB ta ke yi mata.
A cikin bidiyon, Ms Mmesoma ta yi iƙirarin cewa daga shafin intanet na JAMB ta samu wannan sakamakon.
Ta kuma ƙara da cewa in har akwai kuskure to daga wurin JAMB ne ba daga gare ta ba.
Sai dai a sanarwar da Mr Benjamin ya fitar ranar Talatar nan ya ce JAMB na nan kan bakanta cewa sakamakon na ƙarya ne kuma ba daga shafin hukumar aka samo shi ba.
A duba tambarin QR
Ya ce, “Kowa ya duba tambarin QR da ke jikin sakamakon da ta nuna zai gane cewa mallakin wata ɗaliba ce, Asimiyu Mariam Omobolanle da ta zauna jarrabawar a 2021 kuma ta samu maki 138.
“Bayan haka tun daga 2021 JAMB ta daina sakin sakamakon jarrabawar UTME sai ta haɗa da hoto saboda yawaitar samun ɗaliban da suke musanya sakamakon.
A cewar kakakin na JAMB ya kamata mutane su yi tunanin ya aka yi sakamakon duk waɗanda suka zauna jarrabawar a 2023 ya fito da hoto sai na Ms Mmesoma ne kaɗai babu hoto?
An taɓa a 2021
Mr Benjamin ya ce ko a 2021 an samu wani ɗalibi John Chinedu Ifesanchi da laifin sauya sakamakon jarrabawarsa.
Ya ce “Har wasiƙa ya rubuta wa hukumar JAMB ya na neman diyyar Naira biliyan biyu amma daga baya shi da lauyoyinsa suka ɓige da bai wa hukumar haƙuri bayan da taka kafa hujja gaban hukumomin kare haƙƙin ƴan ƙasa na Najeriya.
Ya ƙara da cewa yanzu haka hukumomin tsaro na bincike domin gano wanda ya kitsa wannan badaƙalar sauya sakamakon na Ms Mmesome kuma a shirye JAMB take ta zauna da wakilan ɗalibar da hukumomin tsaro da na kare haƙƙin bil Adama a gaban mutane domin warware matsalar.