JAMB ta dakatar da sakamako dubu 111 da 981
Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB ta fitar da sanarwa inda ta ce tana shakkar sakamakon jarabawar dubu 111 da digo 981 na wadanda suka zauna jarabarwar UTME ta shekarar 2018 har sai bayan ta kammala bincike. Wata sanarwa da shugaban sashen wayar da kan jama’a na hukumar, Dokta Fabian Benjamin […]

Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB ta fitar da sanarwa inda ta ce tana shakkar sakamakon jarabawar dubu 111 da digo 981 na wadanda suka zauna jarabarwar UTME ta shekarar 2018 har sai bayan ta kammala bincike.
Wata sanarwa da shugaban sashen wayar da kan jama’a na hukumar, Dokta Fabian Benjamin ya fitar ya ce “bayan nazarin dukkan na’urorin sirrin da aka makala a dakunan jarabawar bayan ganawa da masu duba daliabn da masu sanya ido an saki sakamako miliyan daya da budu 502 sannan an dakatar da sakamako dubu 111 da 981”. Inji shi.
Sanarwa ta nuna cewa daukacin mutum miliyan daya da dubu 652 ne suka yi rajistar jarabawar inda hukumar za ta saki sakamakon mutum dubu 112 da 331 tare da na masu lalurar gani guda 350.