JAMB ta kayyade mafi karancin makin samun gurbin karatu a bana

JAMB ta ce babu tilas jami’o’in su yi amfani da mafi karancin makin da ta kayyade.

JAMB ta kayyade mafi karancin makin samun gurbin karatu a bana

Jami’ar Bayero ta Kano, BUK

Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire a Najeriya, ta kayyade maki 140 a matsayin mafi karancin makin samun gurbin karatu a jami’o’in kasar a bana.

Hakazalika, JAMB ta sanar da maki 100 a matsayin mafi karancin makin shiga makarantun kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi.

Shugaban JAMB na kasa, Farfesa Ishaq Oleyede ne ya bayyana yayin ganawa da manema labarai ranar Asabar a Abuja.

Sanarwar na zuwa ne bayan kammala taron fitar da ka’idodin samar da guraben karatu da ke gudanar a babban birnin na Najeriya.

Sai dai Farfesa Oleyede ya ce babu tilas jami’o’in kasar su yi amfani da mafi karancin makin da hukumar ta kayyade wajen bai wa dalibai guraben karatu.

Aminiya ta ruwaito cewa, kimanin masu neman shiga makarantun gaba da sakandare 1,595,779 ne suka zana jarrabawar JAMB a bana.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan