JAMB ta sake fitar da sakamakon ɗalibai 36,540

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta fitar da karin sakamakon jarabawar dalibai 36,540, wadanda a baya aka rike. Wannan ya biyo baya ga sakamakon jarrabawar dalibai 531 da aka fitar a makon da ya gabata, wanda ya kawo jimillar sakamakon da aka fitar zuwa 1,879,437. Mai magana da yawun hukumar ta […]

JAMB ta sake fitar da sakamakon ɗalibai 36,540

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta fitar da karin sakamakon jarabawar dalibai 36,540, wadanda a baya aka rike.

Wannan ya biyo baya ga sakamakon jarrabawar dalibai 531 da aka fitar a makon da ya gabata, wanda ya kawo jimillar sakamakon da aka fitar zuwa 1,879,437.

Mai magana da yawun hukumar ta JAMB, Dr. Fabian Benjamin, ne ya sanar da hakan da yammacin jiya Talata.a

Ya ce: “An fitar da sakamako 531 kwanan nan. Har yanzu ana ci gaba da bincike kan wasu da aka gano sun nuna rashin da’a wasu kuma sun yi satar jarrabawa.

“Domin haka hukumar za ta so ta duba  hotunan da na’urar daukar hoto ta CCTV da aka sanya a duk cibiyoyinta da aka amince da ita don tantance gaskiyar abin da ya faru”

Kakakin hukumar ya bada tabbacin yi wa ‘yan Najeriya bayanin abin da suka gano da zarar sun kammala binciken.

Hukumar ta ƙaryata zargin da ake na cewa an mata kutse a shafin adana bayananta ta intanet, ta kuma ce bata shirin sa wadansu dalibai da ake kan duba sakamakonsu maimaita jarrabawar.

Hakazalika hukumar ta kore zargin bacewar sakamakon jarrabawar da ta yi na shekarar 2024 da sauran shekarun da suka gabata.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta