JAMB ta rike sakamakon jarabawar dalibai 64,624
JAMB ta saki sakamakon jarabawar 2024 amma ta soke lasisin wata cibiyar jarabawarta a Jihar Kano
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB) ta rike sakamakon jarabwar dalibai 64,624 da suka zana jarabawa a bana (2024).
A ranar Litinin Shugaban JAMB, Farfewa Ishaq Oleyede ya sanar da hakan yana mai cewa an rike sakamakon ne domin gudanar da bincike, saboda wasu dalilai.
Farfewa Ishaq Oleyede ya bayyana haka ne a lokacin da yake sanar da sakin sakamakon jarabawar ta UTME 2024.
A cewarsa, “Cikin sakamakon jarabawa 64,624 da aka rike 2,896 suna da matsalar tantancewa; 4,594 kuma matsalar rashin bin ka’ida ne; sai wasu 57,056 masu alkala da bincike a cibiyar da suka yi jarabawa. Akwai kuma 78 da ake bincikar su kan laifin jarabawa.”
Farfesa Oloyede ya kara da cewa duk da haka, hukumar ta saki sakamakon dalibai 1,842, 464 daga cikin dalibai 1,904,189 da suka zana jarabwar ta UTME a tsawon kwanaki shida.
A cewarsa, kashi 0.4 daga wadanda suka zana jarabawar sun samu maki sama da 300, sannan kashi 24% suka samu maki akalla 200.
Sai dai ya ce, duk da haka dalibai 80,810 sun yi fashin zana jarabawar.
Hukumar a cewarsa, ta soke lasisin cibiyar zana jarabawarta da ke makarantar, Makama School of Technology, da ke Bichi a Jihar Kano saboda rashin yin aiki yadda ya kamata.