JAMB ta soke cibiyoyin jarabawa 22 masu damfara

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta soke rajistar cibiyoyin 22 na rubuta jarabawarta ta intanet (CBT) masu damfarar dalibai. JAMB ta ce cibiyoyin sun yi damfara ta sama da Naira miliyan 59 daga dalibai 11, 823 ta hanyar karbar fiye da N200 da aka sanya na yin gyara a bayanan dalibai. “Wasu na […]

JAMB ta soke cibiyoyin jarabawa 22 masu damfara

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta soke rajistar cibiyoyin 22 na rubuta jarabawarta ta intanet (CBT) masu damfarar dalibai.

JAMB ta ce cibiyoyin sun yi damfara ta sama da Naira miliyan 59 daga dalibai 11, 823 ta hanyar karbar fiye da N200 da aka sanya na yin gyara a bayanan dalibai.

“Wasu na karbar N3,000 zuwa N5,000 daga dalibai; abin da kuka karba ya haura Naira miliyan 59” inji shugaban hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede.

A lokacin da yake ganawa da masu cibiyoyin a ranar Alhamisa, ya ce hukumar na da kwararan hujjoji ta hanyar yin rajista da neman sauyin bayanai a cibiyoyin da abun ya shafa.

Ya kuma ce suna kin amfani da bayanan sirrin da aka ba kowannensu wajen yin gyare-gyaren.

Oloyede ya kuma yi garagadin cewa duk cibiyar da ta ba wadanda aka dakatar din bayanan sirrinsa, to shi ma za ta dakatar da shi.

Hukumar a cewarsa, ta soke sauye-sauyen da aka yi wa dalibai a cibiyoyin ba bisa ka’ida ba, kuma za ta ajiye musu kudaden da suka biya ta na sauye-sauyen da aka damfare su, za ta kuma gurfanar da masu cibiyoyin a gaban kotu.

Don haka ya bukaci dalibai da aka soke cibiyoyin da suka yi rajista da su sauya bayanansu na sirri da suka ba wa cibiyoyin.

Oloyede ya bayyana damuwa cewa, “Cibiyoyin sun futo ne daga yanki daya ne” na Najeriya kuma hakan hadari ne ga kasar.

Tattaunawar ta kuma caccaki masu cibiyoyin da suka saba ka’idojin hukumar da na kariyar COVID-19 a wurin yin rajistar dalibai.

Mai daya daga cibiyoyin, ya dora laifin a kan ma’aikatansa wadanda ya ce ya sallama.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos