JAMB ta soke mafi karancin makin shiga manyan makarantu na bana
Yanzu dai makarantun ne ke da wuka da nama wajen yanke makin.
Dalibai na zana jarabawar JAMB
Hukumar da ke Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta soke mafi karancin makin da za a bukaci dalibai su samu kafin a basu gurbin karatu a manyan makarantun kasar nan.
Hakan dai na nufin yanzu hukumar ta ba makarantun wuka da nama wajen yanke yawan makin da kowaccensu take bukata ga dalibi kafin ta ba shi gurbin karatun a cikinta.
- Kurunkus: Jirgin karshe dauke da dakarun Amurka ya bar Afghanistan
- E-Naira: CBN Na Shirin Kaddamar Da Kudin Intanet
Hukumar dai ta dauki matakin ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki na 2021 da ya gudana ta intanet ranar Talata.
Taron dai ya gudana ne karkashin jagorancin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu.