Jamhuriyar Kwamin-titi
A makon da ya arce mun yi bita kan jerin gurgun ci gaban da kasar Haurobiya ta samu, a matsayint ana dunkulalliyar kasa da ta shekara babban lauje da kofar hanci da samun ’yanci, amma shagabanni na kassarata, inda suka kware da kwashi-kwaraf, domin suna kallon kansu tamkar ’yan ci-rani. Shi yasa tunda aka dawo […]
A makon da ya arce mun yi bita kan jerin gurgun ci gaban da kasar Haurobiya ta samu, a matsayint ana dunkulalliyar kasa da ta shekara babban lauje da kofar hanci da samun ’yanci, amma shagabanni na kassarata, inda suka kware da kwashi-kwaraf, domin suna kallon kansu tamkar ’yan ci-rani. Shi yasa tunda aka dawo da mulkin dama-dama-da-kurda-kurdar wasoson Samson-siya-siya ’yan ci-rani ke ta cin rani babu kakkautawa.
Daminar siyasa ta zame wa Haurobiyawa damuwa, inda ’yan ci-rani suka yi wa kasar nan babban rauni; su kuwa masu kaka-gida, suka sanya al’amura suka yi kiki-kaka. Kowa ya san yadda Sususun wawan Makurda ya nuna gazawa wajen warware kiki-kakar asusun ilimi. Turken Kabawa ya turke matsalar haramta Bobo da kwambon bokoko. Kuma Rubdigau ya bankado badakalar wasoson man tunkuza, amma an wancakalar da shi.
Kai ko so ake yi a mayar da kasar nan Jamhuriyar Kwamin-titi? Da zarar shagabanni sun sha gaban al’umma, sun aikata tabargaza da tafka ta’asa a kwanon tasa, sai akwai a asassa musu kwamin-titi, wai ta haka za a shawo kan tsillin matsalolin da suka addabi al’umma. Sabanin gyara, kullum sai a karke da ’yan yare-gyare irin na gyare da kurege.
Batu na ingarman karfe, kwamin-titi da ake ta kakkafawa a kasar Haurobiya babu abin da suke haifar wa kasar nan illa kara kassara al’umma da dagula al’amura. Domin na tuna da abokaina direbobin alli, wadanda ke hankoron shiga tsallen badake irin na jiga-jigan asusun ilimi.
Duk wani mai karatun wasikar jakin-dawa da na gida, an dagula masa kidaya, domin mujallu da makalu da jaridu ba sa bayar da haske kan yadda za shawo kan Halin-burtu: A bada kama, a yi barna; Ga ’yan uwan da ba su –da –wani, wadanda suka kware wajen cin basussukan wuni-wuni. Matasa masu jini a jika, su kuwa an kirkiro musu Yawon-wuni-wuni.
Haurobiya, mu roki Mai-duka, mu yi wa dabi’unmu garambawul, mu rage kwasar gararumar jar-miya. Wajibi ne tun daga matakin unguwanni zuwa birane, a kafa tarkon gafiya da jaba da kusu, har ma da su burgu, don a hana su wadaka.
Kowa ya san cewa tun da kasar nan ta zama Jamhuriyar Ja-ni-ina-reto, Haurobiyawa ke fama da duhun dundumdurundum. To idan ta zama Jamhuriyar Kwamin-titi, ibna za mu samu kanmu a ciki nan wasu jerin shekaru babban lauje da kofar hanci?
Ba don gudun kada ku ce ina darasi, ina wasanninmu na dodanni ba, aid a sia in ce ku shawarci yaron can GizBaba ya bar cikin kango, domin yanzu mahukunta a Haurubja bin kangwaye suke suna dirka wa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba alburushi. Sai dai wannan ba laifinsu ba ne. Domin kauran Baubawan-cici ya ce me yasa kuka shigo Haurubja, garin da aka gina, domin masu hannu da shuni da masu rike da mukamai a gwamnatance.
A kasar nan idan ka ci karo da dan gidan Maidan taku da kulki, musamman idan kana jan linzamin kurkurido a manyan tituna, wajibi ne ka tanadi Hauro karamin lauje da zagaye, idan ba haka ba kuwa, to za a sanya ka dan tsahirta. Shi kuwa wand aya tafka ta’asa, ko me dauke da kayan laifi, da zarar ya biya, sai kawai ya wuce fiyu!
Wai yaushe Haurobiya za ta ci gaba, ko da irin na mai gina kwakware ne? mhm! Ba haka nike nufi ba. Wai ina so in ce yaushe za ta kamo dayadaga cikin damisoshin Asiya, wato kasashe irin su Tayar-Landan da Malalen-suya da Indon-isiya. Kai ina fargabar kada Zamajn-gidan-buwai ta zo ta yi mana fintinkau. To ga dai Niyar-jari nan da ke cikin Hamada ta fara ba mu man tunkuza da kuli-kuli!
Masu mulki a kara kwazo wajen bikin ranar ‘’yan ci-rani, a daina wani Dodorido da ranar ’yanci. To kun ji! Ehe!
’Yan makaranta masu koyon watsattsake da buda wagagen litattafai, ya kamata ku rika bin kadin labaran Banga-da-gadi da Tarbar-bunu da Zanen-nashe da Dalilin-taronsu da Gadin-yana da Ladar-shafi da Faffale-dalili da Balon-faranti, uwa-uwa da amintattar jarida ta kasar Haurobiya. Tunda kowa ya san sai an ci kilishi, a murguda baki, a kuma kanga gilashi, sannan a yi ta yaren Ingilishi, lallai akwai bukatar kowa ya mallaki gatarin faskaren ma’anoni.
Ku kuwa masu kwakwazo da watsattsake, ina kira gareku da ku ji tsoron Mai-duka, ku daina karbara ‘Yasar tankin-yuyu.’ Ku yi wa al’umma hidima wajen bayyana batutuwa na ingarman karfe. Kuma a matsayina na Babban direban alli, ya kamata in jero muku manyan misalai a aikace. Don haka na rage yawan surutu rututu kamar Kamfanin dillancin Labarai na Reuers!