Jami’a na sanya dalibanta su kwanta a kabari don tuna Lahira

Jami’ar Radboud da ke birnin Nijmegen a kasar Holland, tana tutiya da wani “kabari na tsarkakewa” da take da shi da dalibai kan kwanta a cikinsa na tsawon awa uku don su yi tunanin abin da ya dace da su. Wannan  “kabarin tsarkakewa” na Jami’ar  Radboud ya yi kama da sabunta tsarin nan na shiga […]

Jami’a na sanya dalibanta su kwanta a kabari don tuna Lahira

Wani mutum ya kwanta a cikin kabari

Jami’ar Radboud da ke birnin Nijmegen a kasar Holland, tana tutiya da wani “kabari na tsarkakewa” da take da shi da dalibai kan kwanta a cikinsa na tsawon awa uku don su yi tunanin abin da ya dace da su.

Wannan  “kabarin tsarkakewa” na Jami’ar  Radboud ya yi kama da sabunta tsarin nan na shiga halwa don yin tunanin abin da ya dace da mutum da mabiya darikun Sufaye ke yi. An gina rami ne a shekarar 2009  kuma ya kasance a cikin aikin da ake gabatarwa na cika ka’idojin kasancewa a aji na biyu wanda aka daina yi a shekarar 2011. Amma a yanzu tsarin ya sake dawowa a bana, saboda yadda dalibai suke ta kiraye-kirayen a maido da tsarin.

Daliban jami’ar da daliban Jami’ar Kimiyya ta HAN mai makwabtaka da jami’ar  suna rubutawa cewa suna son a bar su su kwanta a cikin kabarin na tsawon minti 30 zuwa a wa uku  kuma ba a amincewa su shiga cikin kabarin da wayoyin hannu ko wani littafi, wanda hakan zai ba su damar mayar da hankali a kan tuna zaman barzahu da lahirarsu.

“Tunda yake batun rayuwa da mutuwa suna daya daga cikin abubuwan da ake tattaunawa yau da kullum, mun sake gina wani kabari a cikin lambu inda za ka iya kwantawa,” inji shafin Intanet  na Jami’ar  Radboud .

“Kai da kanka ne za ka yanke tsawon lokacin da kake so ka shafe a kabarin. An hana shiga da waya ko littafi. Haka kuma za ka iya daukar wurin a matsayin wani wuri mai muhimmanci. Kasarka kasa ce sama kuma samaniya. Daga nan kai da kanka za ka iya gane inda ka dosa. Ka shirya wa hakan? Amma idan kuma ba ka son kwanciya a kabarin za ka iya zama kawai a kan benci a gefen kabarin,” inji sanarwar

Dalibai 39 ne kacal suka yi wannan kwanciya a tsakanin 2009 – 2011, amma yanzu da aka sake gina kabarin a watan Yuli dalibai da dama  ne suka halarce shi. Wani dalibi mai suna Ilse Hubers wanda  sakatare ne a coci ya bayyana wa jaridar Bice Magazine cewa “Yanzu jama’a sukan ziyarci kabarina kai a kai wadansunsu suna cewa “sun samu cikaken hutu a cikinsa,” yayin da wadansu kuma suke cewa “Abin ya tayar masu da hankali.”

“Babu wani abu da zai dauke maka hankali a wurin. Kawai za ka kwanta ne a ciki sannan ka fara tunani,” inji wani dalibi mai suna Feona Kane. “Ka san mutane kan ce sun samu wata irin natsuwa a yayin da suka je bayan daki, ta yadda har sukan manto wayoyin hannu ko wani abu, to wannan ma kamar haka yake, sai dai bambancin kawai a nan ka ajiye su ne da sani.”

John Hacking, dalibin coci kuma wanda ya gina “kabarin tsarkakewa” ya ce kwanciya a kabarin ba yana nufin an mutu ba ne kuma ba yana nufin ka yi mutuwar gangan ba ce, amma wata dama ce ta yin wani tunani a rayuwarka.

Sanya wa mutane tunanin mutuwa ya kasance wata hanya ta magance wasu cututtuka a baya. A 2017 mun rubuta labarin wadansu matan China da suka yi amfani da “magani ta hanyar kwanciya a kabari” don yin maganin damuwar da takan biyo bayan  rabuwar aure Haka kuma shekara biyu kafin hakan mun kawo labarin “Kwatanta yaya mutuwa za ta kasance” wanda aka rika koya wa daliban da ke fama da matsalar damuwa a kasar Koriya ta hanyar sanyawa su kwanta a cikin akwatin gawa.

NAJERIYA A YAU: Haƙiƙanin Dalilan Nasarar APC A Zaben Gwamnan Edo

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu