Jami’an asiri na DSS na satar bayanan layukan wayar Tinubu – Kyaptin Sagir Koli

Kyaptin Sagir Kooli sojan da ya bayyana faifan bidiyon yadda aka murda zaben Jihar Ekiti a makon da ya wuce, ya ce jami’an asirin na DSS suna satar nadar bayanan layukan wayoyin Tinubu.Jam’iyyar ta yi zargin cewa an yi amfani da sojoji an kama shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Ekiti a lokacin da aka gudanar […]

Jami’an asiri na DSS na satar bayanan layukan wayar Tinubu – Kyaptin Sagir Koli
Jami’an asiri na DSS na satar bayanan layukan wayar Tinubu – Kyaptin Sagir Koli

Kyaptin Sagir Kooli sojan da ya bayyana faifan bidiyon yadda aka murda zaben Jihar Ekiti a makon da ya wuce, ya ce jami’an asirin na DSS suna satar nadar bayanan layukan wayoyin Tinubu.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa an yi amfani da sojoji an kama shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Ekiti a lokacin da aka gudanar da zaben gwamna a jihar a kwanakin baya.
Sanarwa ta bayyana yin amfani da sojojin a matsayin ‘wani mataki da gwamnatin da ta karaya ta shirya don tsorata ’yan adawa’.
Jam’iyyar ta ce yayin da gwamnatocin kasashen Chadi da Niger suka tura sojojinsu don yaki da ’yan kungiyar boko haram, ita kuwa gwamnatin tarraya  tana amfani da sojojinta wajen tsorata ’yan adawa.
Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce sojoji dauke da makamai na shawagi a gidansa kwanaki uku da suka wuce.
Tinubu ya bayyana cewa ya hango sojoji su kimanin 30 a cikin mota a kusa da gidansa da ke unguwar Ikoyi da misalin karfe 11 na daren ranar Lahadi.
Tinubu ya ce jibge sojoji a kofar gidansa ba zai sanya ya daina ci gaba da kiran a bi doka da oda ba.
Da yake mayar da martani kwamandan runduna ta 81 ta sojojin Najeriya da ke jihar Legas, Manjo Janar Tamubomiebi Dibi ya yi watsi da zargin da Tinubu ya yi.
Ya ce ‘Wannana zargi ne wanda ba shi da tushe bare makama, a ce sojoji na shawagi a gidan Bola Tinubu. Babu wani dan siyasa a Jihar Legas da muke bibiyarsa’.
Ya bayyana cewa akwai rundunar jami’anmu wadanda ake yi wa lakabi da OP Mesa da kRG da ke aiki a yankin Ikoyi da bictoria Island don tabbatar da tsaro.