Jami’an Cibil Defence sun kama masu fasa bututun mai a Filato

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Cibil Defence ta kama masu fasa bututun mai su biyar ciki har da jami’an tsaro biyu a Deport da ke kusa da Jos babban birnin Jihar Filato. Kwamandan Hukumar a jihar Mista bencent Bature ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos. Ya […]

Jami’an Cibil Defence sun kama masu fasa bututun mai a Filato
Jami’an Cibil Defence sun kama masu fasa bututun mai a Filato

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Cibil Defence ta kama masu fasa bututun mai su biyar ciki har da jami’an tsaro biyu a Deport da ke kusa da Jos babban birnin Jihar Filato. Kwamandan Hukumar a jihar Mista bencent Bature ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos. Ya ce sun samu rahoton masu fasa bututun mai a Deport, nan take suka je wurin suka kama  mutum biyar suna wannan aika aika.Ya ce biyu daga cikin mutanen jami’an tsaro ne. Kwamandan ya ce sun mika jami’an tsaron zuwa ga hukumomin da suke aiki, don su yi bincike su gurfanar da su a gaban kotu. Ya ce mutum ukun kuma wadanda farar hula ne  sun gurfanar da su a gaban kotu. Har ila yau Kwamandan ya ce sun samu nasarar kama wani mutum mai sayar da ruwa a garin Jos mai suna dan Kurama, bisa zargin yana datse ruwan da ake turowa daga madatsar ruwa ta Yakubu Gowon zuwa unguwannin Dilimi da Jami’ar Jos yana sayar wa jama’a. Ya ce sun riga sun gurfanar da mutumin a gaban kotu. Mista Bature ya ce suna samun nasarori ne sakamakon hadin kan da sauran jami’an tsaro da al’umma ke ba su. Ya ce ko masu fasa bututun man da suka kama sojoji ne suka taimaka musu, don haka ya yi kira ga jama’a su ci gaba da ba su hadin kai ta hanyar kai rahoton masu fasa bututun da masu satar kayan wutar lantarki.