Jami’an DSS da masu gadi sun ba hamata iska a asibiti

An ba hamata iska tsakanin jami’an hukumar tsaro ta DSS da jami’an tsaron wani kamfani a Asibitin Kwararru na Jihar Edo da ke Benin.

Jami’an DSS da masu gadi sun ba hamata iska a asibiti

Jami’in hukumar DSS

An ba hamata iska tsakanin jami’an hukumar tsaro ta DSS da jami’an tsaron wani kamfani a Asibitin Kwararru na Jihar Edo da ke Benin.

Jami’an DSS din sun tayar da kura ne bisa zargin ma’aikatan asibitin da kin duba wani jami’in hukumar da aka kawo shi bayan ya yanke jiki ya fadi a lokacin da suke tsaka da taro a wurin aiki.

A garin haka ne rikici ya kaure, inda aka ji wa wasu mutane da dama rauni, ciki har da jami’an kamfanin tsaron da wata jami’ar sibil difens da ke aiki a asibitin.

Sai da aka kira ’yan sanda da Babban Dogarin Gwamna Jihar daga baya suka kwantar da kurar.

Wani jami’in DSS ya shaida wa wakilinmu cewa suna cikin mitin ne abokin aikin nasu ya yanke jiki ya fadi, suka kawo shi asibitin, wanda shi ne mafi kusanci da ofishin nasu.

“Amma ba su karbe mu yadda ya kamata ba. A mota muka kawo abokin aikinmu namu.

“Ya kamata idan aka kawo mara lafiya asibiti a duba shi, amma tun daga mota suka fara cewa ba za su dauke shi ba, sai dai mu fito da shi daga motar.”

Amma shugaban asibitin, Dokta David Odiko, ya ce ma’aikatan asibitin sun duba wanda aka kawon a kan kari, amma da likita ya shaida musu cewa ya riga ya rasu tun kafin a kawo shi, sai sai suka ki yarda.

Ya ce “Ba na nan, sai kira na aka cewa ga abin da ke faruwa, amma ko da na zo asibitin sun tafi, sai ’yan sanda na samu.

“Sun kawo shi ranga-ranga cewa ya yanke jiki, kuma likitan da ke aiki ya yi masa duk abin da ya kamata, sannan ya shaida musu cewa ya riga ya rasu tun kafin a zo asibiti.
 “Amma suka ce ba za su yarda ba, suka ajiye shi a kasa, daga baya wasu abokan aikinsu suka shigo, har wata jami’ar Sibil Difens da ke aiki a lokacin suka ji wa rauni  a kanta.” in ji shugaban asitbitin.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume