Jami’an EFCC sun kai samame ofishin Namadi Sambo
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC), sun kai samame wani ofishin tsohon Mataimakin Shugaban kasa da ke Abuja. Jami’an sun yi tsinke wa ofishin Namadi Sambo a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 12:00 na rana inda suka kai har karfe 6:00 na yamma suna bincike a ciki kamar […]
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC), sun kai samame wani ofishin tsohon Mataimakin Shugaban kasa da ke Abuja.
Jami’an sun yi tsinke wa ofishin Namadi Sambo a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 12:00 na rana inda suka kai har karfe 6:00 na yamma suna bincike a ciki kamar yadda wata majiya da ke da alaka da samammen ta shaida wa Aminiya.
Ofishin yana kusa da ofishin Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) da kuma Kwalejin Tsaro na kasa (NDC) da ke tsakiyar Abuja.
Majiyoyi sun ce samamen yana da alaka da binciken da ake yi kan karkata kudin sayo makamai da ake zargin tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Kanar Sambo Dasuki da rarraba kaso mai tsoka daga cikin Dala biliyan 2.1 ga ’yan siyasa domin yakin neman zabe ga tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben da ya gabata.
Bayanai sun ce an kai samame ofishin Namadi Sambo ne domin gano takardun da ake jin sun alakanta tsohon Mataimakin Shugaban kasar da kudin makaman.
Majiyoyin Hukumar EFCC sun ce masu bincike suna da yakinin cewa wasu kudaden da aka raba domin kamfe din siyasa daga ofishin Dasuki sun bi ta ofishin tsohon Mataimakin Shugaban kasar.
Bayanai sun ce an kwashe takardun mu’amala da bankuna da wasu kayayyaki a yayin samamen. Kuma majiyar EFCC ta ce hukumar tana kara tsananta bincike kan harkokin kudi na tsohon Mataimakin Shugaban kasar sakamakon zarginsa da yin amfani da dukiyar kasa wajen gudanar da kamfe.
An ce jami’an EFCC sun kuma ziyarci gidajen Sambo a garuruwan Kaduna da Zariya don ci gaba da bincike.
Mataimakin Shugaban kasar dai ba ya kasar nan na tsawon lokaci, to amma wasu majiyoyi sun ce ya dawo.
Lokacin da Aminiya ta ziyarci gidansa na Zariya a farkon wannan mako ta ga ’yan sanda kalilan da suke gadin gidan. Kuma sun ki amsa tambayoyinta inda suka babu wanda zai iya ba mu bayani.
Shi ma Kakakin Sambo, Malam Umar Sani ya ki cewa komai lokacin da wakilinmu ya tuntube shi. “Ba zan ce komai ba, saboda jaridarku ta riga ta buga labari kan lamarin kafin ta tuntube mu don jin ta bakinmu. Don haka ba zan ce komai ba.”