…Jami’an gwamnatin Jang ba sa tsoron EFCC – Pam Ayuba

Aminiya: Me za ka ce kan rahoton da kwamitin da Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya kafa, wanda ya yi zargin gwamnatinku da tafka almundahana?Pam Ayuba: Wato rahoton kwamitin wanda Mataimakin Gwamnan Jihar Filato Farfesa Sonni Gwanle Tyoden ya gabatar wa Gwamna Simon Lalong, rahoto ne wanda babu gaskiya a cikinsa. Domin babban abin da […]

…Jami’an gwamnatin Jang ba sa tsoron EFCC – Pam Ayuba
…Jami’an gwamnatin Jang ba sa tsoron EFCC – Pam Ayuba

Aminiya: Me za ka ce kan rahoton da kwamitin da Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya kafa, wanda ya yi zargin gwamnatinku da tafka almundahana?
Pam Ayuba: Wato rahoton kwamitin wanda Mataimakin Gwamnan Jihar Filato Farfesa Sonni Gwanle Tyoden ya gabatar wa Gwamna Simon Lalong, rahoto ne wanda babu gaskiya a cikinsa. Domin babban abin da ya bai wa kowa mamaki shi ne babu komai a cikin rahoton sai zargin cewa an ci kudi. Don haka rahoton ya nuna cewa dama can akwai wani abu a cikin zuciya. Gwamnatin da ta gabata ita ma ta kafa kwamiti wanda tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Shedrack Best ya shugabanta, kuma ya ba da rahoto kan yadda gwamnatinmu ta tafiyar da jihar a cikin shekara takwas da ta yi, wanda aka mika musu. Idan da sun duba rahoton ba za su yi irin wadannan zarge-zarge ba. Don haka wannan ya nuna cewa su babu abin da suka kulla sai sharri. Kuma wannan sharri ba zai kai su ko’ina ba, haka mu ma ba zai kai mu ko’ina ba. Abin da al’ummar Jihar Filato suke bukata a wannan lokaci shi ne a yi musu ayyukan da aka yi alkawari a lokacin yakin neman zabe. Amma ba kullum a tsaya ana zarge-zarge cewa an ci kudi an ci kudi ba. Su wane ne suka ci kudin, idan suka yi bincike sai su fitar da sunayen wadanda suka ci kudin. Kafin a zargi mutum a tabbatar cewa ana da hujoji tukuna.
Aminiya: Wato dukkan zarge-zargen da aka yi wa gwamnatinku a cikin rahoton kwamitin ba gaskiya ba ne?
Pam Ayuba: Ko kusa babu gaskiya a cikin zarge-zargen da aka yi. Domin kundin rahoton kwamitin da gwamnatinmu ta kafa, wanda ya mika musu mulki yana da shafuka 188. Su kuma a wannan kwamiti nasu, sun sanya mutum 188 saboda haka kowane mutum yana da shafi daya ke nan a cikin rahoton da muka mika musu. Ya kamata su tsinto wasu abubuwa masu amfani a cikin rahoton da muka mika musu.
Gwamnatinmu ta ce ta bar bashi na Naira biliyan 103, a cikin wannan kudi akwai basussukan da gwamnatin ta gada daga gwamnatin Dariye, wanda shi Gwamna mai ci ya yi Shugaban Majalisar Dokokin Jihar a lokacin. A lokacin bashin da ake bin jihar nan, sai da ya kai Naira biliyan 80. Idan ka dubi wannan bashi da gwamnatinmu ta gada na Naira biliyan 80 daga gwamnatin Dariye, sai ka ga bashin da muka bari bai taka kara ya karya ba. Ayyukan da gwamnatinmu ta yi suna nan a bayyane babu wani abin tsoro, domin mun san mun yi aiki. Don haka muna nan, duk wanda yake cewa zai zo ya yi aiki fiye da mu ya zo ya yi mu gani, amma ba wai a yi ta zargin cewa mun bar bashi ba.
Aminiya: Amma gwamnatin ta ce kun bar bashin Naira biliyan 222 da miliyan 300 ne ba Naira biliyan 103 ba?
Pam Ayuba: Wannan magana mafarki ne, idan suna da gaskiya su sayi shafukaa jaridu, su sanya rahoton kwamitin da muka ba su a gefe daya kuma sanya nasu rahoton a gefa daya, domin jama’a su yi alkalanci.
Aminiya: To a yanzu an ce an ba ku mako biyu ko dawo da kudaden da ake zargin kun ci yaya za ku yi?
Pam Ayuba: Akwai ’yan kwangiyar da suka yi ayyukan da muka bayar sai su je su tambaye su. Idan akwai wanda ya tafi da kudade sai su kama shi. Ai sun ce sun yi bincike kuma bincikensu ya nuna musu an ci kudade.
Aminiya: Wato a takaice wannan rahoto bai tayar muku da hankali ba?
Pam Ayuba: Tashin hankali na me? Wane ne ya yi sata da za a ce ya mayar da kudi?. Ai akwai hanyoyin da doka ta ce a bi. Ba sun ce za su kawo EFCC da ICPC ba? Su zo muna nan muna jiransu babu wanda zai gudu ya bar Jihar Filato. Domin babu wanda zai ji tsoron wai gwamnati Lalong za ta sanya hukumar bincike ko ta kawo EFCC ko ICPC. Na san EFCC da ICPC ba zakuna ne da za a ji tsoronsu ba. Muna nan daram duk kwamishinonin da suka yi aiki a gwamnatin Jang suna nan daram a Jihar Filato suna barcinsu lafiya babu inda za su je.
Aminiya: To Wane sako kake da shi ga al’ummar Jihar Filato kan wannan dambarwa da take faruwa?
Pam Ayuba: Mutanen Filato sun san abin da ke faruwa, suna gani yanzu wata biyu ke nan da zuwan wannan gwamnati ta Lalong, amma babu abin da ta kulla. Sai dai sharrance-sharrance. Ya kamata su dukufa su yi wa al’ummar Jihar Filato aiki.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu