Jami’an Gwamnatin Tarayya sun gana da ‘yan fim a Kano

Jami’an aiwatar da shirin Gwammnatin Tarayya kan tallafa wa masana’antar shirya fina-finai na Najeriya mai suna ProjectAct Nollywood sun gana da masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa. An gudanar da taron na yini daya a zauren taro na otel din Tahir da ke Kano a ranar Larabar makon jiya.Shugaban shirin kuma jagoran […]

Jami’an Gwamnatin Tarayya sun gana da ‘yan fim a Kano

????????????????????????????????????

Jami’an aiwatar da shirin Gwammnatin Tarayya kan tallafa wa masana’antar shirya fina-finai na Najeriya mai suna ProjectAct Nollywood sun gana da masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa.
An gudanar da taron na yini daya a zauren taro na otel din Tahir da ke Kano a ranar Larabar makon jiya.
Shugaban shirin kuma jagoran jami’an gwamnatin Tarayya, Dokta Supo ya ce makasudin taron shi ne don a tattauna da ’yan masana’antar shirya fina-finan Hausa da kuma jin shawarwarinsu dangane da yadda shirin ProjectAct Nollywood zai tallafa wa harkar kasuwancin fina-finai, kasancewarsa daya daga cikin manyan rukunan da ke rike da masana’antar fina-finan Hausa kuma wanda aka ware wa kaso mai tsoka na Naira miliyan 200 na tallafi don samun nasararsa.
An dai gabatar da jawabai daga bangaren masu aiwatar da shirin na gwammnati tarayya a kan matsayarsu da inda aka kwana tun da aka kirkiro shirin.
Mahalarta taron ‘yan fim kamar Ali Nuhu da Iyantama sun gabatar da tambayoyinsu na wasu abubuwa da suka shige musu duhu da kuma korafe-korafe na yadda ake gudanar da shirin tare da yadda yake tafiyar hawainiya da kuma dorewarsa da kuma sauran bukatu na musammnan daga masu shirin fim a Arewacin kasar nan, wanda ya bambanta da na Kudanci .
Cikin manyan bakin da suka halarci taron akwai Ministan Ma’aikatar Al’adu wanda ya samu wakilcin wata Darakta daga ma’aikatar. Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya samu wakilcin Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano Farfesa Umar Faruk Jibrin.
‘Yan fim din da suka halarci taron akwai Hauwa Maina da Hamisu Lamido Iyantama da Ali Nuhu da Isa Ja da Ishak Sidi Ishak da Ibrahim Mandawari da Habibu Sani da Salisu Mohammed Officer da Jamilu Ahmed Yakasai da Marubuta kamar su Balaraba Ramat da sauran mahalarta daga jihohin Kaduna da Katsina da Filato.
Shirin ProjectAct Nollywood wani shiri ne da gwamnatin tarayya ta bullo da shi a karkashin kulawar Ministan Kudi da Tsare-tsare, Dokta Ngozi Okonjo-Iweala don tallafa wa masana’antar shirya fina-finai na Najeriya. A karkashin wannan shiri ne gwamnatin ta ware Naira biliyan uku don inganta sana’ar shirin fim saboda la’akari da tasirinsa da kuma irin alfanun da yake kawo wa kasa.
A bayanin da Aminiya ta samu shirin ya karbi kimanin Naira miliyan 700 a shekarar da ta gabata kuma kamata ya yi ayyukan shirin su yi nisa musamman ta hanyar daukar nauyin ‘yan fim don su halarci kwasa-kwasai a ciki da kuma wajen kasar nan amma har yanzu shiru suke ji kamar an shuka dusa, kasancewar tun da aka kirkiro shirin masu ’yan fim din Hausa sun ce su gafara Sa dai ake ta yi musu, amma su ba su ga ko kaho ba, kasancewar a cikin mutane sama da 500 da suka nemi wannan gurbin karatu, mutum goma ne kacal daga ’yan fim din Hausa suka samu shiga tsarin.