Jami’an Hisbah sun cafke matasan da ke buga karta a Kano
Hukumar dai ta yanke musu hukuncin karanta Alkur’ani.
Jami’an hukumar Hisbah a Jihar Kano sun cafke wasu matasan da aka samu suna buga wasan karta a Karamar Hukumar Warawa da ke Jihar.
An dai kama matasan ne a garin na Warawa bisa zarginsu da bata lokacinsu a banza, a maimakon su yi amfani da shi ta wani abin da zai amfanmi rayuwarsu.
- Sojojin Najeriya sun kera jirgin ruwa na yaki
- Kamfani ya ba dan Shugaban DSS kyautar gidan N90m a Abuja
Hakan ne ya sa jami’an hukumar suka raba musu takardun Alkur’ani sannan suka umarcesu da su karanta a matsayin hukunci.
A cikin wata gajeruwar sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook, Hisbah ta ce, “Ofishin hukumarmu da ke Karamar Hukumar Warawa, karkashin Babban Kwamnadan hukumar, Dokta Harun Sani Ibn Sina, ya kama wasu matasa saboda bata lokacinsu wajen buga wasan karta.
“Daga nan ne ofishin ya raba musu wani bangare na Alkur’ani tare da umartarsu da su karanta don su ribaci lokacin nasu,” inji hukumar.
A yan watannin nan dai hukumar ta kuma zafafa da kamen matasan da ke yin askin banza a Jihar, inda take tilasta musu askewa.
Kazalika, a watan Agustan da ya gabata ma Hisbah ta sanar da haramta yin amfani da mutum-mutumi domin yin tallan kayan sa wa, inda ta ce hakan kamar alamar gumaka ce.