Jami’an Hukumar NCCE sun ziyarci Kwalejin Ilimi ta Izala
Ayarin manyan jami’an Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta kasa (NCCE) a karkashin jagorancin Mataimakin Daraktan Hukumar, Mista bitalis Uji sun ziyarci Kwalejin Ilimi da kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa take shirin budewaa Jos. Jami’an sun kawo ziyarar ce don ganin abubuwan da aka tanadar a kwalejin bayan da kungiyar ta […]
Ayarin manyan jami’an Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta kasa (NCCE) a karkashin jagorancin Mataimakin Daraktan Hukumar, Mista bitalis Uji sun ziyarci Kwalejin Ilimi da kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa take shirin budewa
a Jos.
Jami’an sun kawo ziyarar ce don ganin abubuwan da aka tanadar a kwalejin bayan da kungiyar ta rubuta wa hukumar takardar don neman amincewarta da bude kwalejin.
Da yake jawabi Mista bitalis Uji ya ce sun zo sun gane wa idanunsu abubuwan da kuka
tanada a kwalejin ilimin da kuke son ku bude a Jos, kuma wannan ziyara ce ta bayar da shawarwari kan abubuwan da suka gane wa idanunsu. Ya ce “Wannan ba ita ce kwalejin ilimi da za ku fara budewa ba, kuna da irinta a Gombe, kuma kuna da kyakkyawan tsari kan harkokin ilimi a wannan kungiya.”
Ya ce mazaunin makarantar na dindindin da ake ginawa a hanyar Zariya ya dace, kuma ya yi kira ga kungiyar ta yi kokari ta bunkasa wannan wuri. Ya ce za mu sake kawo wata ziyara kafin a fara yaye dalibai a kwalejin. Kuma ya ce wadannan ne matakan da ake bi kafin a amince da bude kwalejin ilimi a kasar nan, kuma ana bin wadannan ka’idoji ne domin samar wa da nagartatcen ilmi a kasar nan.
A jawabin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Sheikh Sani Yahya Jingir, ya mika godiya ga ayarin kan wannan ziyara da suka kawo tare da shawarwarin da suka bayar kan kwalejin ilimin da suke son budewa.
Ya ce “Mun ji shawarwarin da kuka ba mu, kuma mun karbe su da hannu bibbiyu, don haka ina tabbatar muku cewa za mu yi iyakar kokarinmu wajen ganin mun yi aiki da shawarwarin.
Wadanda suke cikin ayarin akwai Farfesa Umar T. Muhammad da Mista Sam Ugwuoti da Mista Uko I. Uko da Misis Lami Dutse da Malam Musa Garba da kuma Misis Mary Bako.