Jami’an ilimi sun haramta amfani da littafin Malala a Pakistan
Jami’an ilimi a kasar Pakistan sun haramta amfani da littafin yarinyar nan mai rajin kare hakkin mata mai suna Malala Yousafzai a dukkan makarantu masu zaman kansu da ke kasar bisa abin da suka kira rashin martaba addinin Musulunci da kuma zama ’yar kore ga Turawan Yamma. Kamfanin Dillancin Labarai na AP wanda a ruwaito […]
Jami’an ilimi a kasar Pakistan sun haramta amfani da littafin yarinyar nan mai rajin kare hakkin mata mai suna Malala Yousafzai a dukkan makarantu masu zaman kansu da ke kasar bisa abin da suka kira rashin martaba addinin Musulunci da kuma zama ’yar kore ga Turawan Yamma.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP wanda a ruwaito haka ya ce Malala wanda sunanta ya fito a duniya bara sakamakon harbinta da aka ce Taliban sun yi a kai a Arewa maso Yamma na Pakistan kan sukar kungiyar game da takaita ilimin ’ya’ya mata a watan Oktoba ne ta wallafa littafin mai suna “Ni ce Malala,” tare da hadin gwiwar wata ’yar jaridar Birtaniya mai suna Christina Lamb.
Sai dai a yayin da Malala ta zama jaruma a idon wasu kasashe akwai zargi a kasarta Pakistan cewa an shirya harbinta ne domin a mayar da ita jaruma domin Turawan Yamma su samun karbuwa a kasar.
Shugaban Kwamitin Gudanar da Makarantu masu Zaman Kansu na Pakistan Malam Adeeb Jabedani, ya ce kwamitinsa ya haramta littafin daga shiga dakunan karatunsa dubu 40, kuma ya bukaci gwamnati ta hana sanya shi a manhajar karatun kasar.
Jabedani ya ce, “Komai game da Malala na fitowa fili a yanzu. A wurina tana wakiltar Yammacin Turai ne, ba mu ba.”
Shugaban Gamayyar Makarantu Masu Zaman Kansu na Pakistan Malam Kashif Mirza, ya ce kungiyarsa ma ta haramta littafi na Malala a duk makarantun da suke da alaka da ita. Mirza ya ce, Malala “A bar misali ce ga yara amma wannan littafi ya kawo shakku game da ita. Ta wannan littafi ta zama karyar farautar Turawan Yamma.”
Ya ce littafin bai girmama Musulunci ba, saboda ya ambaci sunayen Annabi Muhammad ba tare da yi masa salati ba, lamarin daya zame jiki a duniyar Musulmi. Kuma ya ce littafin ya martaba la’anannen marubucin nan Salman Rushdie wanda ya fusata Musulmi da littafinsa Ayoyin Shaidan, inda a ciki ta ruwaito mahaifinta na cewa, “Ayoyin Shaidan ya ci zarafin Musulunci, amma ina matukar goyon bayan ’yancin bayyana ra’ayi. Kamata ya yi mu fara karanta littafin sannan mu mayar da martani da namu littafin.”
A cikin littafin Malala ta kare ’yan Ahmadiyya tare da nuna bacin rai kan yadda ake kai hari ga marasa rinjaye, wadda take nufin Kiristoci, wannan ya sa Musulmin Pakistan ke ganin duk wani abu da ya shafi Malala wani munafunci ne na kasashen Turai.