Jami’an jakadanci sun hana talla da hoton askin Shugaban Koriya ta Arewa
Jami’an ’yan sanda sun shiga tsakanin Jami’an jakadancin Koriya ta Arewa da shagon gyaran gashi, waje hana masu shagon yin tallar salon gyaran gashi ko salon aski irin na shugaban kasarsu, Kim Jong-Un. Masu shagon dai sun yi tallar ne ga masu son salon gyaran gashi, tare da yi musu rangwamen farashi.Mai shagon, Mo Nabbach […]
Jami’an ’yan sanda sun shiga tsakanin Jami’an jakadancin Koriya ta Arewa da shagon gyaran gashi, waje hana masu shagon yin tallar salon gyaran gashi ko salon aski irin na shugaban kasarsu, Kim Jong-Un. Masu shagon dai sun yi tallar ne ga masu son salon gyaran gashi, tare da yi musu rangwamen farashi.
Mai shagon, Mo Nabbach ya bayyana wa jaridar the London Ebening Standard, cewa jami’an jakadancin kasar ’yan gurguzu, masu bin akidar Satalin, sun sauke masa hoton tallar gyaran gashinsa na M&M Hair Academy a unguwar Ealing da ke Yammacin Landan. Sun kuma bas hi umarnin ya cire “hoton cin mutunci” da ya lika, a cewarsa.
Wannan hoto dai yana dauke da Kim da tuntun gashin kansa, inda aka yi rubutu mai taken: “Ranar mummunan gashi – Bad hair day? Akwai ragowar kasha 15 cikin 100 ga duk wanda yake bukatar irin wannan salon gyaran gashin cikin watan Afrilu.”
“Na gaya musu nan Ingila ce, ba Koriya ta Kudu ba, don haka su kirawo lauyoyinsu,” kamar yadda jaridar ta ruwaito daga bakin Nabbach. “Wadannan mutane suna sanye da kwat, kuma da gaske suke a nufinsu. Barazanarsu na da matukar tsoratarwa,” inji shi.
Nabbach, wanda kwararren mai daukar hoto ne, ya ce, tuni ya ce hoton don gudun bacin rai.
’Yan sanda sun tabbatar da cewa sun shiga tsakanin don warware matsalar.
“Jami’an sun gana da sassan da ke rikici da juna, amma ba a bayyana aikata wani laifi ba,” kamar yadda Mai Magana da yawun ’yan sandan birnin Landan, ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
Ofishin Jakadancin Koriya ta Arewa, da ke wajen birnin Landan da kimanin kilomita uku daga inda shagon gyaran gashin yake, bai bayar da wata sanarwa ba.