Jami’an JTF 14 sun samu karin girma a Yobe
Rundunar Soja ta kasa ta ciyar da jami’anta 14 da ke aiki a rundunar tsaron ta musamman (JTF) da ke Jihar Yobe don yaba wa kwazonsu da sadaukar da rayukansu don ganin an samu zaman lafiya a jihar.Da yake makala sababbin mukaman ga jami’an 14, Kwamnadan Rundunar JTF a Jihar Yobe Kanar Ibrahim Sallau ya […]

Rundunar Soja ta kasa ta ciyar da jami’anta 14 da ke aiki a rundunar tsaron ta musamman (JTF) da ke Jihar Yobe don yaba wa kwazonsu da sadaukar da rayukansu don ganin an samu zaman lafiya a jihar.
Da yake makala sababbin mukaman ga jami’an 14, Kwamnadan Rundunar JTF a Jihar Yobe Kanar Ibrahim Sallau ya hori jami’an su ci gaba da ayyukan da suke gudanarwa da suka kai su ga samun karin girma tare da nuna jajircewarsu a kan ayyukansu, kuma su yi amfani da sababbin mukaman nasu wajen ciyar da aikin soja da kasa gaba.
Kanar Sallau ya ce mukaman da jami’an nasa suka samu sun hada da jami’ai tara da aka kara wa girma daga Laftana zuwa Kyaftin sai jami’ai biyar da suka zama cikakkun Laftana.
Da ya ke jawabi a madadin jami’an da suka samu karin girman Kyaftin Barde godiya ya yi ga Allah dangane da wannan matsayi da suka samu tare da gode wa rundunar sojan kasar nan bisa ga la’akari da kwazonsu har ta ciyar da su gaba. Ya ba da tabbacin ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyuka da suke yi na dawo da zaman lafiya a Jihar ta Yobe da kasa baki daya.