Jami’an JTF da UNESCO sun tallafa wa mabukata a Masarautar Godogodo
Kimanin zawarawa da marayu da nakasassu da sauran mabukata 400 ne suka amfana da kayayyakin tallafi da Hukumar Tsaro ta Fararen Hula (Sibiliyan JTF) da hadin gwiwar Hukumar UNESCO suka bayar a Masarautar Godogodo da ke Karamar Hukumar Jama’a a Kudancin Jihar Kaduna. Tallafin, wanda ya kunshi tufafi da sabulan wanka da wanki an raba […]
Kimanin zawarawa da marayu da nakasassu da sauran mabukata 400 ne suka amfana da kayayyakin tallafi da Hukumar Tsaro ta Fararen Hula (Sibiliyan JTF) da hadin gwiwar Hukumar UNESCO suka bayar a Masarautar Godogodo da ke Karamar Hukumar Jama’a a Kudancin Jihar Kaduna.
Tallafin, wanda ya kunshi tufafi da sabulan wanka da wanki an raba su ne ga mabukatan don nuna tausayawa da kuma rage musu radadin rayuwa, kamar yadda Shugaban Hukumar UNESCO a Jihar Kaduna, Dokta Ahmed Khalifa ya bayyana a wajen taron rabawar da aka yi a garin Jagindi Tasha da ke Masarautar Godogodo.
A jawabinsa a wajen taron da aka gudanar a harabar Cocin Katolika na St. Steben da ke garin Jagindi, Dokta Khalifa, wanda shi ne Kwamandan Hukumar Sibiliyan JTF ta Shiyyar Kudancin Kaduna, ya ce wannan tallafi somin tabi ne daga cikin ayyukan da hukumarsu ta sanya a gaba a bana, Inda ya ce daga ciki akwai tallafi na musamman ta bangaren ilimin ’ya’yan marasa galihu da na nakasassu da kuma marayu da za su samu ta hanyar daukar nauyin kashi hamsin na kudin da yaro zai kashe har tsawon shekara uku.
“A kwanakin baya muka kammala da Masarautar Atyap da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf inda muka kashe musu Naira miliyan 18 na tallafin daukar nauyin karatunsu a gundumomi tara na masarautar, inda nan kuma muka tsara kashe Naira miliyan takwas kan bayar da tallafin karo ilimi ga masu rabo cikin mabukata kuma a yanzu haka mun zo muku da takardun da za ku cika bayan mun tantance ku.” inji shi
A karshe ya isar da sakon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ga jama’ar yankin musamman matasa kan nisantar harkokin shaye-shaye, inda ya ce gwamnati ta kuduri aniyar kamawa da rufe shagon duk wanda ta samu yana sayar da kayan maye. Sai ya gargadi shugabannin al’umma musamman sarakuna su guji zuwa gidajen shaye-shaye sanye da rawunna don kada su gamu da fushin gwamnati.
A jawabinsa a madadin Hakimin Godogodo, Malam Musa Bawa, Dagacin Jagindi Tasha, Malam Umar Sale ya nuna godiyarsu da yadda aka tuna da mabukatan da ke masarautarsu da irin tallafin da ake matukar bukata. Sai ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar tallafin a yanzu da wadanda za su samu nan gaba su yi hakuri da abin da suka samu komai kankantarsa domin duk wanda ya tuna da kai a lokacin tsanani to shi ne masoyinka.
Baya ga kayayyakin da aka raba musu kyauta, an kuma gudanar musu da gwaje-gwajen cututtuka tare da raba musu magunguna cikin farashi mai sauki.