Jami’an kashe gobara sun ceto zakara daga rijiya a Kano
Hukumar ta ce ta samu nasarar ceto zakaran da ran shi
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce jami’anta sun sami nasarar ceto wani zakara mai shekara daya daga wata rijiya da ya fada a unguwar Kwalli da ke birnin Kano.
Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyana haka a Kano, inda ya ce sun samu kira daga mazauna unguwar kuma tuni suka amsa kira tare da ceto zakaran da ransa.
Ya ce, “Mun samu kiran gaggawa daga wani mai suna Kamalu Garba da misalin 10:12 na safe, inda ya sanar da mu faruwar lamarin.
“Nan take jami’anmu suka isa wajen, inda suka tarar wani zakara mai kimanin shekara daya ya fada rijiya. Daga bisani mun yi nasarar ceto shi cikin koshin lafiya,” inji shi.
Kakakin ya kuma ce tuni suka mika zakaran zuwa ga mai shi, wato Abdullahi Umar da ke unguwar ta Kwalli.
Ya kuma yikira ga jama’ar Kano da su guji barin rijiyoyi a bude domin gudun faruwar makamancin hakan.