Jami’an MDD A Nigeria Sun Yi Jimamin Mutuwar Abokan Aikinsu A Gaza
Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya sun yi juyayin abokan aikinsu da aka kashe a yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza
Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya sun bi sahun takwarorinsu na duniya wajen yin shiru na minti daya domin juyayin abokan aikinsu da aka kashe a yakin da Isra’ila da Hamas ke ci gaba da yi a Gaza.
A ranar Litinin Ofishin Majalisar na Najeriya ya yi wannan juyayi ta hanyar yin kasa-kasa da tuta, a yayin da ma’aikata a ofisoshinsu a fadin duniya suka yin shiru na minti daya “domin girmama abokan aikinmu da aka kashe a Gaza.”
Mukaddashin Babban Jami’in Majalisar Dinkin Duniya kuma mai kula da ayyukan jin kai a Najeriya, kuma Wakilin Shirin Ci Gaba na Majalisar Dinkin Duniya, Mohamed Yahya, ne ya bayyana haka a lokacin takaitaccen taro da aka saukar da tutar Majalisar a ofishinta da ke Abuja.
Ya bayyana cewa “an saukar da tutar Majalisar Dinkin Duniya ne a matsayin alamar girmamawa,” ga wadanda suka rasu.
- Najeriya Za Ta Binciki Soke Bizar ’Yan Kasarta 264 Da Saudiyya Ta Yi
- Yajin aiki: Gwamnati ta gayyaci NLC domin tattaunawa
“Ina kira ga dukkanmu da mu yi shiru na tsawon minti daya domin girmama abokan aikinmu da suka mutu,” in ji shi, yana mai jaddada muhimmancin tunawa da wadanda suka sadaukar da kansu wajen hidimta wa bil’adama.
A hukumance, jami’ai 86 da ke halartar taron koli na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya da ke gudana a jihar Neja sun yi shiru na minti daya.
Da misalin karfe 1:30 na rana, mahalarta taron sun tashi don yin shiru na minti daya don girmama abokan aikinsu da suka mutu a Gaza.
Bayan shirun na minti dayan ne, Yahaya ya kammala saƙon nasa da fatan alheri: “Allah Ya sa sun huta.”