Jami’an NDLEA da b.I.O za su fara kama direbobi ’yan kwaya
Sabon Daraktan Hukumar Kula da Lafiyar Ababen Hawa (b.I.O) na Jihar Bauchi Injiniya Muhammed Binni Abdulkadir ya ce nan da kwanaki kadan jami’an hukumarsa da hadin gwigwar Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a jihar za su fara kama direbobin da suke tu’ammali da miyagun kwayoyi a lokacin da suke tuki.Injiniya […]
Sabon Daraktan Hukumar Kula da Lafiyar Ababen Hawa (b.I.O) na Jihar Bauchi Injiniya Muhammed Binni Abdulkadir ya ce nan da kwanaki kadan jami’an hukumarsa da hadin gwigwar Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a jihar za su fara kama direbobin da suke tu’ammali da miyagun kwayoyi a lokacin da suke tuki.
Injiniya Binni ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa a garin Bauchi a ranar Alhamis din makon jiya.
Injiniya Binni ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya haramta mutum ya sha kwaya a lokacin da yake tuka abin hawa, saboda haka daga yanzu duk direban da suka samu yana wasa da rayuwar al’umma ta hanyar shan kwaya lokacin tuki zai dandana kudarsa.
“Domin yanzu da ni da sabon Shugaban Hukumar NDLEA mun kulla wata yarjejeniya na kama masu shan kwaya a daukacin kananan hukumomin jihar nan 20,” inji shi.
Ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga direbobin jihar su rika kiyaye dokokin tuki kuma wadanda lasisin tukinsu ya kare su sabunta su kafin su shiga hannun hukuma.