Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50
Jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) sun aika mayaƙan Boko Haram kimanin 50 lahira a yayin musayar wuta a Jihar Kaduna.
Jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) sun aika mayaƙan Boko Haram kimanin 50 lahira a yayin musayar wuta a Jihar Kaduna.
Hukumar NSCDC ta bayyana cewa mayaƙan na Boko Haram sun gamu da ajalinsu ne bayan sun kai wa jami’anta harin kwanton ɓauna ranar Litinin.
Kakakin Hukumar NSCDC, Babawale Afolabi, ya ce jami’an hukumar sun yi arangama da mayaƙan ne a lokacin da suke zagayen sintirin kare babban layin wutar lantarki da ya taso daga yankin Shiroro ne a Jihar Neja.
“Mayaƙan Boko Haram kimanin 200 ɗauke da muggan makamai ne suka kai wa jami’an kusan su 80 hari a yankin ƙauyen Farin Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Cikin da ke Jihar Kaduna.
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno
- DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya
- Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi
“Daga ganin ayarin motocin jami’an suka buɗe wa musu wuta wai saboda zargin ayyukan jami’an tsaron sun takura musu a yankin.
“Amma jami’an namu sun yi nasarar halaka mutum 50 daga cikin maharan, ko da yake ba a ga mutum bakwai daga cikin jami’an namu ba tukuna. Akwai wasu kuma da suka samu raunuka a yayin musayar wutar,” in ji shi.