Jami’an SSS sun kama wadanda suka kashen yaron da suka sace a Kano
Jami’an Hukumar Tsaron kasa (SSS) sun yi nasarar kame mutanen da ake zargi da sacewa tare da hallaka wani yaro dan shekara biyar mai suna Aliyu Aminu a Unguwar Na’ibawa a birnin Kano.An gano gawar Aliyu wanda aka sace a ranar Talatar makon jiya lokacin da yake dawowa daga makarantar Islamiyya ne a wani gini […]
Jami’an Hukumar Tsaron kasa (SSS) sun yi nasarar kame mutanen da ake zargi da sacewa tare da hallaka wani yaro dan shekara biyar mai suna Aliyu Aminu a Unguwar Na’ibawa a birnin Kano.
An gano gawar Aliyu wanda aka sace a ranar Talatar makon jiya lokacin da yake dawowa daga makarantar Islamiyya ne a wani gini da ba a kammala a ranar Laraba bayan an biya diyyar Naira miliyan biyu a asusun banki na wadanda suka sace shi.
Aminiya ta samu labarin cewa mamallakin asusun da aka tura kudin yana cikin wadanda aka kama. Kuma an gano cewa an kama daya daga cikin wadanda suka sace yaron a ranar Alhamis a birnin Kano ta daya daga cikin hanyoyin wayar da aka yi amfani da shi wajen kulla yarjejeniyar biyan fansar. A lokacin kulla yarjejeniyar fansar wadanda suka sace yaron sun yi amfani da lambobin waya daban-daban har guda bakwai.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa layi na farko da barayin yaron suka yi amfani da shi na wani dalibin jami’a ne. Kuma dalibin ne ya rika lura da yadda aka gudanar da lamarin.
“Jami’an SSS sun amshi lambar daga mahaifin yaron suka tafi kamfanin sadarwar layin inda suka gano adireshin dalibin,” inji majiyar. Kuma ta kara da cewa ta wannan adireshi ne jami’an SSS suka samu nasarar kama wasu mutanen da suka bayar da adireshin dalibin.
“An kama dalibin a gidansu a Kano, kuma ya yi ikirarin aikata laifin. Shi ne wanda ya tsara yadda aka kama sauran mutum uku da ake zargi. Kuma an kama jagoransu ne a Kaduna,” inji majiyar.
Daraktan Hukumar SSS na Jihar Kano Mista Basset Eting ya tabbatar da kamun inda ya ce nan gaba kadan za a gabatar da wadanda ake zargi ga manema labarai.