Jami’an tsaro a tashi tsaye
Makonni biyu ke nan tun bayan da aka sace dalibai ’yan mata a garin Chibok da ke Jihar Borno, wadanda har yanzu ba a san halin da suke ciki ba. Abin bakin ciki da takaici, sai ga labari na ta yaduwa (wai) an tsallaka da wasu daga cikin ’yan matan ta tafkin Chadi. Alhali a […]
Makonni biyu ke nan tun bayan da aka sace dalibai ’yan mata a garin Chibok da ke Jihar Borno, wadanda har yanzu ba a san halin da suke ciki ba. Abin bakin ciki da takaici, sai ga labari na ta yaduwa (wai) an tsallaka da wasu daga cikin ’yan matan ta tafkin Chadi. Alhali a makon jiya ne muka ji cewa wadanda suka sace matan sun aurar da wasu. Abin kamar almara, tun iyayen matan na sa ran jami’an tsaro za su iya kubutar da ’ya’yansu har suka fara mika lamarin ga Mai yin yadda Ya so.
Don Allah ina jami’an tsoron Najeriya? Mene ne aikinsu? Ko dai zargin rashin kwarewar da ake yi musu gaskiya ne? Shin ta yaya wadanda ake zargin ba a san ko su wane ne ba za su shigo cikin makaranta su saci akalla mata 200, ba tare da an gan su ko an san su ba? Gaskiya akwai lauje a cikin nadi. Don satar mutun 200 ba satar kudi ba ce.
Yau da a ce Sarakuna da Gwannoni, Sanatoci da shuwagabannin al’umma za su yi ko da barazanar bin barayin matan ne (kamar yadda iyayen daliban suka yi), na tabbata da jami’an tsaro sun dauki abin da muhimmanci. Amma a cikinsu babu wanda ya yi ko da dogon kashedi ga jami’an tsaron, ballantana su dauki abin da muhimmanci. Mun tabbata da ace akwai ‘yayan wani Sarki ko Gwannan ko Sanata, da yanzu an sa jami’an tsaro sun shiga dajin tun kafin a tsallaka da su Chadi, duk kuwa da duhun wurin.
Wajibi ne jami’an tsaro tun daga kan Sojoji da ‘yan sanda su san cewa, kare rayuka da dukiyoyin al’umma a karkashin su yake. Kamar yadda suke kare lafiya da dukiya rayukan Sarakuna da gwamnoni da ‘’yan majalisar kasa. To haka yakamata su rika kare na Talakawa.
Ya Allah ka bayyanar da matan da aka sace, ya Allah ka zaunar da kasar mu lafiya, ka karemu daga dukkan batagari, ka ba mu shugabanni adilai amin.
Kabir Sakaina Layin ‘Yangoro Malumfashi. 08095968366