Jami’an tsaro ke ba wa ’yan ta’adda makamai —Ribadu
Nuhu Ribadu ya ce jami’an tsaro ke ba wa ɓata-gari makaman da ake ta’addanci da su a Najeriya
Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce jami’an tsaro ke taimaka wa ’yan bindiga da sauran ’yan ta’adda da makamai.
Ribadu ya bayyana cewa yawancin makaman da ake aikata laifi da su a Najeriya sun shiga hannun ɓata-garin ne ta hannun baragurbin jami’an tsaro.
Amma ya yi gargaɗin cewa duk jami’in tsaron da aka kama da hannu a irin wannan laifi na rashin kishin ƙasa, to zai yaba wa aya zaƙi.
Nuhu Ribadu ya sanar da haka ne a taron bikin lalata makaman da suka lalace a Barikin Sojoji na Muhammadu Buhari da ke Abuja.
- NAJERIYA A YAU: Fashewar Tankar Mai: Asarar Da Al’ummar Majiya Suka Tafka
- ’Ya’yana 4 da almajirai 5 sun rasu a gobarar tankar man Jigawa
- Kisan Hanifah: Abdulmalik ya ƙalubalanci hukuncin kisan da aka yanke masa
An ƙona makamai 2,400 da suka ƙunshi lalatattu da tsofaffi da kuma waɗanda aka ƙwato daga hannun masu laifi, a yayin bikin na ranar Alhamis.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Musa da manyan hafsoshin soji sun halarci taron.
Aminiya ta ruwaito cewa sau 23 ana kama tulin makamai na biliyoyin Naira da aka yi fasakwaurinsu zuwa Najeriya a shekaru bakwai da suka gabata.