Jami’an tsaro sun ƙaurace wa zaɓen ƙananan hukumomin Kano

Jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da na sibil difens sun ƙaurace wa tituna da kuma rumfunan zaɓe a yayin da Kanawa suka nufi rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri’arsu a zaɓen ƙananan hukumomin jihar a yau Asabar. Wakilinmu ya lura cewa, yayin da tituna suka kasance fayau babu ko motsin ababen hawa, mazauna […]

Jami’an tsaro sun ƙaurace wa zaɓen ƙananan hukumomin Kano

Jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da na sibil difens sun ƙaurace wa tituna da kuma rumfunan zaɓe a yayin da Kanawa suka nufi rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri’arsu a zaɓen ƙananan hukumomin jihar a yau Asabar.

Wakilinmu ya lura cewa, yayin da tituna suka kasance fayau babu ko motsin ababen hawa, mazauna kuma sun kiyaye dokar hana zirga-zirgar da gwamnatin jihar ta shimfiɗa.

Har ila yau, yayin da masu kada kuri’a ke shirin kada kuri’unsu, tuni kayayyakin zaɓen sun isa wasu rumfunan zaɓen.

Sai dai jami’an tsaro na cikin gida ne kawai da suka haɗa da jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA) da jami’an tsaro na Kano da ‘yan banga ne ke aikin sanya ido kuma a halin yanzu suna bakin aikinsu na tabbatar kiyaye doka da oda.