Jami’an tsaro sun ba da umarnin rufe kasuwar Orlu

Sai dai ba a san dalilin da yasa jami’an tsaro suka bada umarnin ba.

Jami’an tsaro sun ba da umarnin rufe kasuwar Orlu

Hankula sun tashi a yankin Orlu na Jihar Imo yayin da jami’an tsaro suka umarci ‘yan kasuwa da su rufe shaguna na tsawon mako guda.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, umarnin rufe shagunan da jami’an tsaron suka bayar ya biyo bayan gurfanar da Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu a da aka yi a Abuja ranar Litinin.

  1. Rahoton Sahara Reporters ya fusata dubban musulmai
  2. CBN ya haramta sayar wa ’yan canji Dala

Daya daga cikin ‘yan kasuwar wanda ya yi magana da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce galibi  ‘yan kasuwar dillalai ne na katako da kayayyakin gini a kan titin Orlu a Owerri, babban birnin Jihar.

Ya ce, “Mun je shagon da safiyar yau (Litinin) sai muka tarar da sojoji na sintiri a kan titin Orlu zuwa Owerri kusa da kasuwar katako ta Orlu, lamarin da ya sanya ba mu samu damar bude shagunanmu ba.

“Sun ce mu koma gida na tsawon mako  daya.

“Da muka tambaye su dalili, sai suka ce mu koma gida kawai.”

Kazalika, bayanai sun ce hakan ya haifar da cuncurindon ‘yan kasuwa da masu wucewa a kan titin mai cike da hada-hada.

Sai dai kuma wasu na zargin kisan wani DPO na ofishin ‘yan sandan Omuma da wasu mutane shida da ake zargin mambobin IPOB ne ya haifar da rikici a Owerri, babban birnin Jihar Imo.

Kisan DPO din ya auku ne a ranar Litinin yayin da ‘yan awaren IPOB suka yi yunkurin kai hari yankin Omuma da ke Karamar Hukumar Oru ta Gabas kafin a fatattake su.

Sai dai a ranar Talata, ‘yan sanda dauke da manyan makamai sun yi ta sintiri a manyan tituna a cikin kwaryar birnin da kewaye.

Kakakin ‘yan sandan Jihar, CSP Mike Abattam, bai samu damar yin bayani game da lamarin ba.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50