Jami’an tsaro sun bindige wanda ake zargi dan Boko Haram ne a Kaduna

Ranar Lahadi jami’an tsaro sun kashe wani mutum mai suna Usman bisa zargin dan Boko Haram ne a Layin Sarki a Unguwar Kinkinau da ke Kaduna.Jami’an tsaron sun kuma yi awon gaba da dan uwan mutumin bayan sun yi harbe-harbe na tsawon sa’a daya da su.Aminiya ta jiyo cewa a jami’an tsaron da suka hada […]

Jami’an tsaro sun bindige wanda ake zargi dan Boko Haram ne a Kaduna
Jami’an tsaro sun bindige wanda ake zargi dan Boko Haram ne a Kaduna

Ranar Lahadi jami’an tsaro sun kashe wani mutum mai suna Usman bisa zargin dan Boko Haram ne a Layin Sarki a Unguwar Kinkinau da ke Kaduna.
Jami’an tsaron sun kuma yi awon gaba da dan uwan mutumin bayan sun yi harbe-harbe na tsawon sa’a daya da su.
Aminiya ta jiyo cewa a jami’an tsaron da suka hada da na farin kaya da sojoji sun zo ne daga wata jiha domin kama wanda suke zargin, inda suka biya ta Unguwar Rigasa suka kama abokin marigayin kafin su je gidansa a Kinkinau domin kama shi.
Hakimin Unguwar Ma’azu, Cikasoron Zazzau, Alhaji Ahmed Aliyu Idris ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce ya sha gargadin masu gidaje a yankinsa cewa su tabbatar sun binciki mutum kafin su ba shi haya.
Har zuwa hada wannan rahoto Rundanar ’Yan sandan Jihar Kaduna ba ta yi bayani kan da abin da ya faru. Sai dai wata majiya a hedikwatarta ta ce suna da bayanin shigowar jami’an tsaron don wannan aiki.