Jami’an tsaro sun buqaci agaji wajen kame masu sojan gona

Kwamitin tsaro na Jihar Legas da ya  hada da rundunonin rukunonin soja da ’yan sanda,  a taronsu na wata-wata, sun bukaci jama’ar gari su rika ba da tasu gudunmuwa wajen tafiyar da harkokin tsaro,  musamman wajen fallasa mutanen  da ke sojan gona.Da yake wa taron manema  labarai jawabi, jim kadan da kammala taron, kwamamdan sojan […]

Jami’an tsaro sun buqaci agaji wajen kame masu sojan gona
Jami’an tsaro sun buqaci agaji wajen kame masu sojan gona

Kwamitin tsaro na Jihar Legas da ya  hada da rundunonin rukunonin soja da ’yan sanda,  a taronsu na wata-wata, sun bukaci jama’ar gari su rika ba da tasu gudunmuwa wajen tafiyar da harkokin tsaro,  musamman wajen fallasa mutanen  da ke sojan gona.
Da yake wa taron manema  labarai jawabi, jim kadan da kammala taron, kwamamdan sojan sama,  mai kula da bataliya ta 9 da ke unguwar Ikeja, Birgediya-Janar Adeniyi Oyebade  ya ce samar da tsaro ba aiki ne na gwamnati kadai ba,  ko kuma  masu  saye da  kayan sarki, kowane dan kasa na da rawar da zai taka  wajen  ingata matakan tsaro.
Kwamandan ya ce daya daga cikin manya-manyan kalubalen da jami’an tsaro ke fuskanta, musamman  a Jihar Legas, sau tari  sai ka taras  da mutane sanye da kayan sarki suna sojan gona,  suna aikata ayyukan assha.,
Ya ce  sau tari sukan  kama mutane  masu ikirarin ma’aikatan  tsaro ne, amma da an zurfafa  bincike, sai ka taras karya suke yi, masu sojan gona ne. “Gwamnatin Legas  na kokari wajen yakar ayyukan ta’addanci wajen taimaka wa  jami’an tsaro  da dukkan  abin da zai inganta  aikinsu, lamarin da ke kara wa jami’an kwarin gwiwar gudanar  da ayyukansu. Taron  manema  labarai da  ake yi  wata-wata yana agazawa wajen sanar da  jama’a irin  rawar  da  ake  bukatar su  taka  game da  harkokin tsaro”. Inji shi.
Kwamanda  Oyebade  yace da  taimakon naurar  zamani  irin  su  wayan  salula mutane  na  iya  daukan hoton duk   wani  mai sanye da  kayan sarki da  suke  tuhumar  cewa  sojan gona  ne, kuma idan suka  gane cewa  sojan gaskiya  ne amma  irin shigar da yayi  baiyi  kama da  na  maaikacin sarki ba  to zai  huskanci hukunci  dai dai da yadda  dokar  soja tace a hukunta wanda ya wulakanta  kayan sarki.
Dangane da inda sojan gonar  ke samun kayan sarki, kwamandan ya ce  da  yawansu  suna saye ne hannun ’yan fasa-kwabri.  An nuna wa  manema  labarai  kayayyakin  sarki  iri daban-daban  da kuma  lokacin da ake sa kowanne daga  cikinsu.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, kwamandan rundunar sojan sama mai kula da  sashe  na 435, Kwamando Sunday Wukangha ya  bayyana  yadda  kowanne soja ya kamata  ya sa  mukaminsa.  Idan aka samu kuskure a wajen rataya mukamin, ana  iya  gane cewa sojan gona  ne, ana  iya  damke shi ko kuma a dauki hotonsa,  a mika wa ’yan sanda, wadanda za su gudanar da  bincikensu.