Jami’an tsaro sun dakile Boko Haram daga mamaye Damaturu
Da safiyar Litinin da ta gabata ce al’ummar garin Damaturu suka fara jin amon manyan bindigogi da rugugin tashin bama-bamai a garin. Harin wanda ya faro ta bangaren titin Gujiba, jami’an tsaro sun maida martani tare da dakushe yunkurin maharan. Gidan gwamnatin jihar, ofishin hukumar zabe (INEC), Jami’ar Jihar Yobe, hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC) da […]
Da safiyar Litinin da ta gabata ce al’ummar garin Damaturu suka fara jin amon manyan bindigogi da rugugin tashin bama-bamai a garin.
Harin wanda ya faro ta bangaren titin Gujiba, jami’an tsaro sun maida martani tare da dakushe yunkurin maharan. Gidan gwamnatin jihar, ofishin hukumar zabe (INEC), Jami’ar Jihar Yobe, hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC) da ofishin ’yan sanda na garin, suna daga cikin inda ’yan bindigar suka kai wa farmaki.
Wata majiya daga jami’in tsaro a gidan gwamnatin jihar wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana wa wakilinmu cewa: “Har sun yi nasarar shiga cikin gidan gwamnati, sun dangana da babban dakin taron gidan amma cikin taimakon Allah mun fi karfinsu ta hanyar amfani da jiragen yakinmu kuma da dama a cikinsu sun mutu.”
A lokacin da gumurzun ke gudana, Gwamna Ibrahim Gaidam ba ya cikin jihar. Jama’a da dama sun yaba kokarin jami’an tsaron JTF tare da na SSS da sauransu. Kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida mana: “Gaskiya a want ton karon mun yaba da kokarin jami’an tsaro bisa wannan namijin kokari na takaita ta’adin wannan hari da aka kawo a Damaturu.”
Gefe guda kuma, wasu bayanai daga Jami’ar Jihar Yobe sun nuna cewa wannan harin ya tilasta dole daliban makarantar fantsama daji don tsira da rayukansu amma ’yan bindigar sun yi kokarin banka wa mazaunin malaman jami’ar wuta duk da hakan bai yuwu ba.
Jami’in tsaron da muka zanta da shi ya shaida mana cewa: “Amma dai mun kwace duk wuraren da maharan suka yi kokarin mamayewa ta hanyar amfani da jiragen yaki.” Sannan ya kara da cewa duk da ’yan bindigar sun yi iya kokarinsu wajen kai farmaki a sansanin hadin gwiwar jami’an tsaron JTF amma ba su samu nasara ba. Ya ce da dama daga maharan an kashe su, duk kuwa da cewa babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirarin nasu.
Haka kuma wannan harin ya rutsa da wasu kwararrun likitoci biyu, Dokta Mansur da kuma Dokta Hassan Lawan, kamar yadda shugaban kungiyar Likitoci a jihar, Dokta Adamu ya bayyana. Ya bayyana cewa: “Sun rasa rayukansu ne a rukunin gidaje na kan hanyar Maiduguri, daidai lokacin da suke kokarin rakabewa kuma an harbi daya a wuya, dayan kuma a kirji.”
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe, Mista Marcus danladi ya sanar da kafa dokar takaita zirga-zirga ta awanni 24 a babban birni jihar ta Yobe, kodayake an sassauta ta daga shida na yamma zuwa bakwai na safe daga bisani.
Gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Gaidam ya yi Allah wadarai da wannan harin. Bayanin gwamnan ya zo ne ta bakin mai ba shi shawara bangaren yada labaru, Malam Abdullahi Bego. “Kasancewar Gwamna Gaidam ba ya nan wannan al’amari ya faru, yana Abuja domin gudanar da wani aiki na musamman, ya yaba matuka da kokarin jami’an tsaro, wadanda jajircewarsu ta tilasta maharan arcewa kuma Damaturu ta ci gaba da kasancewa karkashin gwamnati.” Inji shi.