Jami’an tsaro sun gano bama-bamai da aka binne a Neja
Kakakin ya ce sun gano abubuwan fashewar ne bayan wani aiki da suka gudanar a jihar.
Jami’an Tsaro a Jihar Neja, sun gano wasu bama-bamai da abubuwan fashewa da yawa a wurare daban-daban da aka binne a wasu yankunan jihar.
Wuraren da aka binne bama-baman sun haɗa da yankin Galadima-Kogo a Ƙaramar Hukumar Shiroro, yankin Mutun-Daya a Karamar Hukumar Munya, da yankin Gbeganu da ke Minna.
- Majalisar ɗinkin duniya ta dakatar da aiki a yankin Deir El-Balah na Gaza
- NNPCL ya fara fitar da iskar gas zuwa China da Japan
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ne, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa an gano abubuwan fashewar ne yayin ayyukan yaki da ta’addanci tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023.
A Galadima-Kogo, wani bam ya tashi a shekarar 2022, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC).
An ɓoye abubuwan fashewar ne a wurare daban-daban, amma tawagar ‘yan sanda tare da sauran hukumomin tsaro a jihar sun gano su, inji kakakin ‘yan sandan.
Abiodun, ya ƙara da cewa an lalata bama-baman a ranar 22 ga watan Agusta, 2024, a bayan Dutsen Zuma da ke Suleja.
Ya ce aikin ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin SP Mohammed Mamun, wanda ke kula da sashen lalata bama-bamai na rundunar.