Jami’an tsaro sun hana jama’a kwasar mai bayan hatsarin tanka a Taraba

Rahotanni sun bayyana cewa faɗuwar tankar man ke da wuya, jami’an tsaron suka isa wurin, inda suka killace wurin domin hana mutane kaiwa inda man yake.

Jami’an tsaro sun hana jama’a kwasar mai bayan hatsarin tanka a Taraba

Jami’an tsaro sun hana mutane zuwa kwasar man fetur daga wata tankar mai da ta yi hatsari a Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba.

A safiyar ranar Litinin ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC), suka ɗauki wannan mataki bayan faɗuwar tankar man a kan babban hanyar Jalingo zuwa Wukari.

Rahotanni sun bayyana cewa faɗuwar tankar man ke da wuya, jami’an tsaron suka isa wurin, inda suka killace wurin domin hana mutane kaiwa inda man yake.

Daga nan ɗauke tankar man da babbar motar ɗauko, aka mayar  wata motar sannan aka tafi da ita.

Kakakin Hukumar NSCDC ne jihar, SC Sam Illiya, ya bayyana wa wakilinmu cewa kwamandan hukumar na jihar da kansa ya jagoranci jami’ansa zuwa wurin domin gudanar da aikin.

Kakakinn ’yan sanda na jihar, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.