Jami’an tsaro sun hana taron kaddamar da littafin tarihin Hausawan Jos

Jami’an tsaro a garin Jos babban birnin Jihar Filato, sun hana taron kaddamar da littafin tarihin Hausawan Jos da aka shirya gudanarwa a Babban Masallacin Juma’a na Jos a ranar Larabar makon jiya.Wakilinmu wanda ya halarci wurin da aka shirya gudanar da taron a ranar LarabaR, ya gane wa idonsa yadda aka girke ’yan sanda […]

Jami’an tsaro sun hana taron kaddamar da littafin tarihin Hausawan Jos
Jami’an tsaro sun hana taron kaddamar da littafin tarihin Hausawan Jos

Jami’an tsaro a garin Jos babban birnin Jihar Filato, sun hana taron kaddamar da littafin tarihin Hausawan Jos da aka shirya gudanarwa a Babban Masallacin Juma’a na Jos a ranar Larabar makon jiya.Wakilinmu wanda ya halarci wurin da aka shirya gudanar da taron a ranar LarabaR, ya gane wa idonsa yadda aka girke ’yan sanda a harabar masallacin. Da yake zantawa da wakilinmu kan mataki da jami’an tsaron suka dauka shugaban kungiyar Jasawa ta kasa Alhaji Shehu Ibrahim Musalla ya ce hana kaddamar da littafin da jami’an tsaro suka yi, “abin da aka saba yi mana ne, domin mu Hausawan Jos a kullum ana hada baki da jami’an tsaro ana kuntata mana da musguna mana,” inji shi. Ya ce dalilan da suka ba su na hana kaddamar da littafi shi ne shi Kwamishinan ’Yan sanda ya ce, “wai mun rubuta wa DPO ne, ba shi muka rubutawa ba, shi kuma ba ya karbar umarni daga wurin DPO sai dai DPO ya karbi umarni daga wurinsa.” Ya ce ba su taba jin cewa duk littafan tarihi da aka rubuta a kasar nan, sai an sanar da kwamishinonin ’yan sanda yankin da aka rubuta littatafan ba kafin a kaddamar da su. Alhaji Shehu Musalla ya ce siyasa ce kawai ta sanya aka hana bikin kaddamar da littafin. daya daga cikin wadanda suka shirya taro Alhaji danladi Garba Pasali ya bayyana wa wakilinmu cewa littafin ya kunshi ainihin tarihin Hausawan Jos. Ya ce an dade ana karyar cewa Hausawa baki ne a garin Jos, inda ya ce littafin ya  nuna Hausawan Jos ba baki ba ne a garin, domin suna nan a gari fiye da shekara 500 da suka gabata. Alhaji danladi Pasali ya ce hana kaddamar da littafin kamar an dada karfafa musu gwiwa ne, domin sun riga sun yi littafin kuma a yanzu mutane suna nan suna ta rububin sayensa. Wakilinmu ya buga wa kakakin rundunar ’yan sandan jihar Felicia Anslem waya don jin ta bakinta kan al’amarin amma bai same ta ba.