Jami’an tsaro sun kara himmar yaki da barayin mai

Wasu da suka kware wajen satar man fetur sun ranta a na kare suka fada cikin teku a lokacin da ’yan sanda suka far musu a ranar Larabar da ta gabata. barayin da suke fasa bututun man fetur a kauyen Akute Ido na karamar Hukumar  Ifo a Jihar Ogun, sun arce suka tsunduma cikin teku, […]

Jami’an tsaro sun kara himmar yaki da barayin mai
Jami’an tsaro sun kara himmar yaki da barayin mai

Wasu da suka kware wajen satar man fetur sun ranta a na kare suka fada cikin teku a lokacin da ’yan sanda suka far musu a ranar Larabar da ta gabata.

barayin da suke fasa bututun man fetur a kauyen Akute Ido na karamar Hukumar  Ifo a Jihar Ogun, sun arce suka tsunduma cikin teku, inda suka bar kananan jiragensu masu injuna hudu da motocin hawa guda bakwai da jarkoki masu cin lita 50 guda 30 dauke da man fetur.
’Yan sandan yankin Ogijo sun yi nasarar kame motar tanka dauke da man fetur wanda aka sato, inda matukin motar ya yi nasarar tserewa a lokancin da ya ankara da  ’yan sandan.
Haka su ma ’yan sandan da ke aiki a garin Shagamu sun yi nasarar kama wata tanka dauke da man fetur na sata a ranar bikin Kirismeti kasa da awa 24 da kame mota ta farko duk a Jihar Ogun. Sai dai a wannan karon an kame barayin, wadanda suka hada da Elochukwu Byron, wadanda a yanzu rundunar ’yan sanda ke tatsar bayanai daga gare su.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun, Abdulmajid Ali, ya yaba wa kokarin jami’ansa, sannan ya sha alwashin ci gaba da jajircewa domin ganin karshen masu fasa bututu suna satar man fetur a jihar. Haka kuma ya yi alkwarin kare rayuka da dokiyoyin al’ummar jihar, inda ya bukace su da su rika taimaka wa ’yan sanda da bayanai domin cimma nasarar yaki da batagari.
Tuni Gwamnatin Tarayya da bayyana aniyarta na sanya Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) da Hukumar Tsaron kasa (DSS) wajen hukunta barayin man fetur ta hanyar fasa bututun man.
 Babbar Manajar Kamfanin Samar da Albarkatun Man fetur da Tallatarwa (PPMC), Esther Nnamdi Ogbue ce ta sanar da haka a lokacin da ta ziyarci daffon man fetur na Mosinmi da bututu man da ke karamar Hukumar Obafemi Owode a Jihar Ogun. A cewarta, shigar wadannan karin hukumomi zai taimaka kwarai wajen hukunta masu fasa bututun da satar mai