Jami’an tsaro sun kashe barayin shanu biyu a Kaduna

Akalla barayin shanu biyu ne hadin gwiwar jami’an tsaro na soja da ’yan sandan da ke garin Saminaka a yankin karamar Hukumar Lere, suka yi nasarar kashewa a yayin wani gumurzu da suka yi a Kaduna. Jami’an tsaron sun kuma yi nasarar kwato shanu 232 daga dajin a lokacin wannan gumurzu.Wannan lamari ya auku ne […]

Jami’an tsaro sun kashe barayin shanu biyu a Kaduna
Jami’an tsaro sun kashe barayin shanu biyu a Kaduna

Akalla barayin shanu biyu ne hadin gwiwar jami’an tsaro na soja da ’yan sandan da ke garin Saminaka a yankin karamar Hukumar Lere, suka yi nasarar kashewa a yayin wani gumurzu da suka yi a Kaduna. Jami’an tsaron sun kuma yi nasarar kwato shanu 232 daga dajin a lokacin wannan gumurzu.
Wannan lamari ya auku ne da misalin karfe 8 na daren ranar Litinin da ta gabata. A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na gwamnatin Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, jami’an tsaron sun samu nasarar ce bayan sun samu bayanin sirri cewa wasu barayin shanu sun iso kauyan Jama’ariya da ke karamar Hukumar Lere, dauke da wasu shanu da ake kyautata zaton na sata ne.
A cewarsa, jin kadan da samun wannan bayani sai jami’an tsaron suka isa kauyan da nufin kama barayin shanun. “Ai da ganinsu sai barayin shanun suka bude masu wuta. Daga bisani jami’an tsaron suka yi nasarar bindige biyu daga cikinsu nan take. Sannan wasu kuma sun tsira da raunuka a jikinsu.
“barayin shanun sun yi watsi da shanun da bindiga daya da rigunan sojoji uku da alburusai 12.” Inji shi.
Aruwan ya kara da cewa, wadannan shanu da aka gano, an mika su a hannun rundunar ’yan sanda da ke Saminaka domin a ci gaba da bincike saboda a gano ainihin masu su. Sannan ya ce ana nan ana ci gaba da bincike, domin gano barayin shanun da suka gudu da raunuka a jikinsu.