Jami’an tsaro sun kashe daliba a garin kama ‘Ƴahoo Boys’’
Jami’an tsaro sun harbe wata dalibar sakandare har lahira a lokacin da suke kokarin kama wasu ’yan ‘Yahoo’
Jami’an tsaro sun harbe wata dalibar sakandare har lahira a lokacin da suke kokarin kama wasu ’yan ‘Yahoo’, masu damfara ta intanet a Jihar Ogun.
Dalibar mai suna Sadiat ta gamu da ajalinta ne a lokacin da jami’an tsaron Operation Mesa suka bude wuta a yayin da suke tsaka da bin ’yan yahoo din.
- An cafke matashi yana yi wa mahaukaciya fyade a Suleja
- Za a gina cibiyar dashen hanta a Kano, wadda babu irinta a Afirka ta Yamma
A garin haka ne harsashi ya sami Sadiat mai shekara 17 a kai a lokacin da suke tafiya da sauran dalibai a gaban makarantarsu.
An garzaya da dalibar da ke aji biyu a babbar sakandare zuwa Babbar Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Idi-Aba a Abeokuta, inda rai ya yi halinsa.
Lamarin dai ya haifar da rudani a yankin Ago Ika da ke garin Abeokuta ranar Alhamis.
Fusatattun daliban makarantar sun yi zuga zuwa ofishin ’yan sanda na Enu-Gada da ke unguwar, suka yi ta yi ta jiran jami’an da ke aiki.
Wani dalibi dan aji daya a babbar sakandare ya yi zargin cewa jami’an tsaron sun yi harbin ne kai-tsaye zuwa cikin dalibai duk da cewa dukkansu suna sanye da kayan makaranta
Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba shi da labarin rasuwar dalibar.
Oyeyemi ya bayyana cewa ba ‘Yahoo Boys’ jami’an tsaron suke bi ba, wani hatsabibin dan kungiyar asiri ne da aka dade ana nema ruwa a jallo.
Ya kuma bayyana cewa an sari wani dan sanda da adda a kai a lokacin yamutsin.