Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 4 a Zamfara
An kuma yi imanin wasu daga cikin ’yan bindigar sun samu raunukan harbin bindiga yayin artabun.
Haɗin gwiwar jami’an ami’an tsaro da ’yan sa-kai da al’ummomi sun hallaka ’yan bindiga huɗu tare da daƙile wasu hare-hare a sassan Jihar Zamfara.
Kakakin ’yan sandan na jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce an gudanar da ayyukan ne a ƙananan hukumomin Birnin Magaji da Bungudu a ranar Alhamis.
Ya ce baya ga kashe mutum huɗu, an kuma yi imanin wasu daga cikin ’yan bindigar sun samu raunukan harbin bindiga yayin artabun.
A cewarsa, harin farko ya faru da misalin ƙarfe 11:30 na safe lokacin da ’yan bindiga suka mamaye gonaki da ke wajen garin Nasarawa Godal a Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji, inda suka fara harbe-harbe kan manoma.
- ’Yan sanda sun ceto mutum 9 daga hannun masu garkuwa a Kaduna
- Hare-haren ’yan bindiga sun tsananta bayan sace Janar Rabe — Al’umma
Sai dai ’yan sanda tare da haɗin gwiwar mazauna yankin sun yi gaggawar tunkarar maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji.
DSP Yazid ya ce an ga jini a hanyoyin da maharan suka bi wajen guduwa, alamar cewa wasu daga cikinsu sun samu raunuka.
Ya ƙara da cewa mutum uku daga cikin mazauna yankin sun samu raunukan harbin bindiga, kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawa.
A wani hari na daban da ya faru da misalin ƙarfe 1:30 na rana, wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Galmar Hannu da ke Gundumar Kekun Waje a Ƙaramar Hukumar Bunguɗu, inda suka riƙa harbe-harbe babu ƙaƙƙautawa.
Jami’an tsaro na rundunar Operation Fansan Yamma da ke yankin sun gaggauta isa wurin bayan samun kiran neman agaji, inda suka fafata da maharan.
A cewar kakakin ’yan sandan, jami’an tsaron sun yi nasarar kashe ’yan bindiga huɗu, yayin da sauran suka tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga. Haka kuma, an ƙwato babur ɗaya da ake zargin na maharan ne.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Ahmad Muhammad Bello, ya yaba wa jami’an tsaro da kuma mazauna yankunan bisa jajircewa da haɗin gwiwar da suka bayar, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen samun nasarar ayyukan.
Ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri, tare da tabbatar musu da cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin hana masu aikata laifuka samun mafaka a jihar.
A nasa ɓangaren, Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana a shafinta na sada zumunta cewa wani artabu tsakanin ’yan bindiga da jami’an sa-kai a garin Nasarawa da ke yankin Bukkuyum ya ɗauki kusan minti 30.
Rundunar ta ce jami’an tsaro biyu sun samu raunukan harbin bindiga a yayin artabun, sai dai ba a rasa ran kowa ba, yayin da jami’an sa-kai suka tsaya tsayin daka har aka fatattaki maharan.